Da ƊUMI-ƊUMI: Za a bai wa maniyyatan Nijeriya guzirinsu a tsabar kuɗi bayan Shettima ya saka baki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A wani yunƙuri na tabbatar da ba a samu tangarda a aikin Hajjin bana ba, Babban bankin Nijeriya (CBN) ya amince da bai wa Hukumar Jigilar Alhazai (NAHCON), tsurar kuɗaɗen guzirin Alhazai don a raba musu a hannu.

Hakan ya biyo bayan tsoma bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya yi kamun-ƙafa da Shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan.

Tun da farko, CBN ya fito da wani tsari na tanadar wa kowane Alhaji katin hada-hadar kuɗi don sauƙaƙa harkokin cinikayya ga maniyyatan a ƙasa Mai tsarki, sai dai hakan ka iya zama ƙalubale musamman ga maniyyatan yankunan karkara waɗanda suka fi sabawa da hada-hadar kuɗi-hannu, wannan ne ya sanya Shugaban ƙasar ya bai wa Babban Bankin umarnin hanzarta komawa amfani da tsarin bayar da guziri na tsaba ga maniyyatan, umarnin da tuni babban bankin ya fara aiki da shi.

Tuni dai NAHCON ta yi maraba da wannan mataki, inda ta bayyana shi a matsayin wata babbar nasara ga yunƙurinta na samar da walwala ga Alhazai, kamar yadda Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda.

“Amincewar da CBN ya yi da komawa tsarin hada-hadar kuɗin tsaba, wani abin farin ciki ne ga alhazan Najeriya, waɗanda a yanzu za su iya gudanar da aikin Hajjinsu cikin sauki” inji hukumar.

Da ya ke zantawa da manema labarai jim-kaɗan bayan ganawarsa da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kwamishinan Kudi na NAHCON, Aliu Abdulrazaq, ya tabbatar da cewa, “Wannan nasarar ta biyo bayan shiga tsakani ne da mataimakin Shugaban ƙasa yayi, inda ya gayyaci mataimakin gwamnan babban bankin ƙasar tare da roƙon su da su yi watsi da batun bai wa maniyyatan katin kuɗin a aikin hajjin 2025, wannan babbar nasara ce ga NAHCON.

“Idan ka je Saudiyya, galibin wuraren da mahajjata ke gudanar da ibadarsu, za ka ga na’urar cire kuɗi mai sarrafa kanta guda ɗaya ce, hakan na haifar da cunkoso da ɓata lokacin ibada, yana da matukar wahala ga mahajjata su iya sayen duk abin da suke so su saya.

“Na biyu, kashi 95 cikin 100 na alhazan Najeriya manoma ne da makiyaya da ba su saba da hada-hadar kuɗin kati ba, kai har tsaba wasunsu kan samu matsala wajen tantance canji.”

“Amma daga yanzu muna da ƙwarin-gwiwa cewa aikin Hajji ba zai zo da cikas ba. Da ma shirye-shirye sun yi nisa sosai, matsalar tsabar kuɗi kudi ce ta rage mana kuma a yau an magance mana ita.”

Ana sa ran ɗaukar wannan matakin zai bai wa alhazan Nijeriya damar mayar da hankali kan ayyukansu na ibada ba tare da sun yi fama da matsalolin kuɗi ba.

By Babaji