
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta bada amsa cikin fushi game da hira da aka yi da alƙalin wasan da zai yi alƙalanci a wasanta da ƙungiyar Barcelona na ranar Asabar, wanda ya fashe da kuka ganin yadda gidan talabijin na ƙungiyar ke matsa wa alƙalan wasa.
Ƙungiyar ta musanta rahotannin da ke cewa ta na shirin ƙaurace wa buga wasan, wanda za a yi da misalin ƙarfe 9 na dare a birnin Seville.
Ricardo de Burgos Bengoetxea shi ne wanda zai yi alƙalancin wasan, wanda kuma shi ne alƙali na ƙarshe da aka tattauna akansa a baya-bayan nan a gidan telebijin ɗin ƙungiyar.
Real Madrid ta ƙi shiga a dama da ita ababan da ake yi gabannin wasa da suka haɗa da buɗaɗɗen atisayen da hira da manema labarai.
A sanarwar da ta fitar a karon ƙarshe, ta ƙaryata jita-jitar cewa ba za ta buga wasan ba, ta na mai cewa ba ta taɓa yunƙurin haka ba.
