Kacaniyar da mu ka sha lokacin da ni da wasu gwamnoni muka naɗa Sarkin Kano – Amaechi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana yadda Ubangiji ya tsare shi a wata tafiya daga Kano zuwa Kaduna lokacin da ya ke gyangyaɗi a yayin tuƙi.

Ya ce, lamarin ya faru ne bayan da shi da wasu sun kammala ƙaddamar da naɗin wani sarki a Kano da bai bayyana sunansa ba.

Tsohon gwamnan na Jihar Ribas ya kuma ce, akwai Goje da Baraje da kuma Farfesa Gambari a lokacin da ya tuƙo motar daga Kano.

Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin taron Gidauniyar Akinjide Adeosun na shekara-shekara da ya gudana a Legas karo na tara .

Ya bayyana cewa, bayan naɗin Sarkin ne, Shugaban Hukumar Ƴan sandan Farin kaya (DSS) a jihar, ya gargaɗe shi da ya fice daga jihar sakamakon akwai barazanar tsaro game zamansa lafiya.

A yunƙurinsa na ficewar ne ta jirgin sama, sai aka faɗa masa cewa an bada umarnin kada a sayar masa da tikitin jirgi sama, lamarin da ya sa ya tuƙo motar.

Ya ƙara da cewa, a lokacin da ya iso Zariya ne sai ya samu damar fitowa don ya kama ruwa, inda daga nan ne suka cigaba da tafiya har zuwa Kaduna, sannan ya samu sararawa.

By Babaji