
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sake bayyana damuwa game da rahoton curewar mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a yankin Tumbus dake Tafkin Chadi da Duwatsun Mandara a Dajin Sambisa dake jihar.
Ya bayyana cewa, an samu koma-baya ta fuskar nasarorin da ake samu a ayyukan sojoji, a ƙoƙarinsu da daƙile ta’addanci a jihar, lamarin da ya sa ƴan ta’addar ɓangarorin biyu suke sake kafa daba a yankunan.
Ya faɗi hakan ne a lokacin da Ministan Tsaro Badaru Abubakar da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya CDS Janar Christopher Musa da wasu manyan kwamandodin soja a ziyarar da suka kai masa a Maiduguri, babban birnin jihar, ranar Juma’a.
Gwamna Zulum ya kuma yaba wa ƙoƙarin sojojin na yaƙi da ta’addanci, saidai ya koka ga yadda suke sake farfaɗowa tare da ƙarfi da suke yi musamman a yankunan Sambisa, ya na mai fargabar akwai yiwuwar ƴan ta’addar su sake karɓe iko da wasu wurare da sojojin suka ƙwato a hannusu a baya.
Haka kuma, Zulum ya tabbatar da cewa, rashin wadataccen kayan aiki ga sojoji shine babban ƙalubalen da suke fuskanta a yaƙin nasu da mayaƙan.
Kazaalika, ya bayyana kaɗuwarsa game da ɗaukar nauyin mayaƙan ɓangarorin, waɗanda ya yi zargin suna samun taimako ne daga ƙasashen waje, wanda ya bayyana a matsayin babban ƙalubale ga gwamantinsu.
Har’ilayau, ya ce matuƙar aka gaza kawo ƙarshen ayyukan mayaƙan a yankin Sahel, to akwai yiwuwar a gaza kashe fitintinun da ke addabar al’umma na tsawon lokaci a shiyyar.
