Daga USMAN KAROFI
Hukumar EFCC ta kama sanannen attajiri kuma mawaƙi, Emeka Okonkwo, wanda aka fi sani da E-Money, a ranar Talata.
E-Money, wanda shi ne Shugaban Kamfanin Emmy Cargoes Nigeria Limited da kuma Five Star Music, an kama shi a Jihar Legas bisa zargin wulaƙanta kuɗin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin E-Money da watsa Naira da Dalar Amurka a wajen wani biki da aka gudanar a Legas, lamarin da ya saɓawa dokokin ƙasar da suka hana irin wannan aiki.
Yayin da ake wallafa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da cafke E-Money.
Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani…
