
Daga BELLO A. BABAJI
A yammacin ranar Talata ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC, ta sako shahararren tauraron nan na Legas, wato Emeka Okonkwo, wanda aka fi sani da E-Money, kwana ɗaya bayan kama shi.
E-Money, wanda shahararren ɗan kasuwa ne, EFCC ta kama shi ne a gidansa dake yankin Omole na Jihar Legas a yammacin ranar Litinin sakamakon zarginsa da laifin wulaƙanta takardar Naira da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje.
Bayan sako shi ne ya sanar da al’umma ta kafar Instagram a daren Talata.
Ya bayyana cewa, ya na cikin ƙoshin lafiya tare da miƙa godiyarsa ga ɗaukacin al’umma ganin yadda suka nuna masa soyayya musamman a lokacin da ya shiga hannun jami’an hukumar.
