Zargin badaƙala: EFCC ta gurfanar da Aisha Achimugu a kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC, ta gurfanar da ƴar kasuwa A’isha Achimugu aka kotu, kamar yadda kotun ta umarta, ranar Laraba.

Jami’ai mata biyu na hukumar ne suka shiga da ita kotun da misalin ƙarfe 11:35 na safe.

Alƙali Iyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya umarci matar, wadda ta fice daga Nijeriya da ta amsar gayyatar EFCC zuwa ƙarfe 12:00 na ranar Talata.

Haka kuma ya umarci EFCC ta gurfanar da ita a ranar Laraba.

Da asubahin ranar Talata ne jami’an EFCC suka kama Attajirar bayan isowarta Nijeriya.

By Babaji