Na shirya taron ZABAFEST ne don farfaɗo da ɗabi’ar karatun littattafai – Maryam Shehu

Spread the love

“Ina burin farfaɗo da ɗabi’ar karatu da al’adunmu na koyo da koyarwa da ƙasar Zazzau” 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Kawo yanzu dai kusan babu wanda bai samu labarin taron bajekolin littattafai da ƙirƙirarrun fasahohi na ZABAFEST da za a gudanar a garin Zariya a ranakun Asabar da Lahadi, wato 26 da 27 ga watan Afrilu, 2025, a birnin Zazzau ba. Sai dai ba kowa ne ya san Maryam Shehu ba, matashiyar da ta ƙirƙiro da wannan taro, irin sa na farko a Zariya Birnin Ilimi. Me ya zaburar da wannan ɗaliba da ke karatun ilimin shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello, don ganin an haɗa wannan taro? Waɗanne abubuwa taron yake so ya tattauna akan su? Kuma wanne ƙalubale take fuskanta wajen haɗa taron? Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da Maryam don jin manufar shirya taron. 

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.

MARYAM SHEHU: Sunana Maryam Shehu. Ni asalin ƴar Zariya ce a Jihar Kaduna. Sannan kuma ni ce shugabar Bookish Alchemy, kamfanin sayar da littattafai da kuma tallafawa marubuta, mawaƙa, da masu basirar zane, musanman na gida, wajen gano basirar su da ba su dama wajen bayyana ta ga duniya.

 Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki?

Kamar yadda na faɗa ni ƴar Zariya ce, marubuciyar labarai da waƙoƙin baka, mai sharhin littattafai da finafinai. Na kammala diploma ta a ɓangaren Shari’a da Dokokin ƙasa (Ciɓil Law) daga Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria. Sannan a yanzu haka ina cigaba da karatun digiri na farko a Tsangayar Nazarin Ilimin Shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello Uniɓersity, Zaria.

 Waɗanne abubuwa ne aka fi saninki a kai?

 Duk wanda ya sanni ya san ina da son rubuce-rubuce, da harkar sayar da littattafai. 

Wacce baiwa ki ke da ita da mutane da dama ba su sani ba?

Bayan ɓangaren karatun boko, rubutu da karance-karance da mutane suka sanni akai, mutane da yawa suna mamakin na san wani abu daga cikin Alƙur’ani Mai Girma. Tabbas, bayan hadda har na koyar tun daga 2018 zuwa 2024 a makarantar koyar da haddar Alƙur’ani. Wannan shi ne abinda da yawa daga cikin mutane ba su sani ba akai na.

Ba mu labarin ZABAFEST, yaya ki ka fara tunanin shiryawa?

ZABAFEST tunani ne wanda nake ɗauke da shi tun a shekarar 2023, amma shawarari daga mutane da abokan arziƙi na nuna cewa abu ne da ke buƙatar kuɗi masu yawa. Don haka abin ya tsorata ni na kau da wannan tunanin. 

Shekara ɗaya bayan haka, kusan ƙarshen 2024 wannan tunani ya dawo min. Ba don ina da kuɗin da suka sa na fasa ba a wancan lokacin, sai dai ina da yaƙinin kamar yadda tunanin ke dawo min za a yi taron da ƴan taro da sisin da nake da shi ko fatan samu wajen ƴan’uwa da abokan arziƙi. Don haka sai kawai na haɗa mutanen da nake ganin za su iya taimaka min, na sanar masu da burina, sai suka goya min baya wajen yin wannan taro.

Daga nan muka fara aiki ka’in da na’in, sai dai cikin abin da ya raunana ni shi ne yadda ake samun ƙarancin samun goyon baya, musamman game da muhimman abubuwan da taron ke buƙata kafin ya kai ga nasara.

Waɗanne abubuwa ne baƙin da za su halarta za su sa ran gani?

Duk wani baƙo da zai halarci taron zai ga matashiya mai ƙaramin shekaru, bahaushiya matsayin wacce ta shirya wannan taro. Akwai tattaunawa akan manyan batutuwa da suka shafi al’adu, fasahohin zamani, littattafai, da kuma waƙoƙin baka daga mawaƙa masu tasowa. Sannan kuma akwai aji na musamman don koyar da rubutun waƙe wanda Poetic Wednesday Initiatiɓe ta ɗauka nauyi. 

Wanne tallafi ko goyon baya ki ka samu, ko ki ke nema don samun nasarar taron?

Haƙiƙanin gaskiya anan dai a Zariya ban samu tallafi daga kowa ba, daga kan ƴan siyasa, ‘yan kasuwa da masu madafun iko, ba kuma don ban nema ba; lokuta da dama na kan yi tunanin cewa ko dai wannan abu ba daidai ba ne ko kuma ba zai kawo cigaba ba ne shi yasa ba wanda ke shirin tallafa min. Sai dai ba zan manta da Malam Abdul’aziz Abdul’aziz ba, Mai Bada Shawara Na Musamman ga Shugaban ƙasa Kan Kafafen Sadarwa Na ɗab’i, kasancewar shi ne mutum na farko da ya tallafa min ta hanyar Aliyu Jalal. Sai kuma Gidauniyar Dr. Bukar Usman, da ta aiko da tallafin kuɗi da kuma littattafai ta hanyar Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ma ya tallafa, sai kuma jaridar Katsina Times.

Tallafi ko goyon bayan da nake nema don samun nasarar wannan taron na da yawa gaskiya, don ka ga akwai kyauta ta Naira dubu 200 da za a bai wa waɗanda za su yi gasar waƙen baka wanda muka ba shi suna Abubakar Imam Poetry Slam.

Su waye suke ɗaukar nauyin taron?

A yanzu dai Allah kaɗai zan ce. Amma har yanzu ban cire tsammanin cewa Allah zai aiko da waɗanda za su taimaka ta inda ban yi tsammani ba.

Yaya ki ke ji da hidimar haɗa wannan taro, dama kin taɓa yi ne? Mene ne ƙalubalen da ki ke fuskanta?

Ba zan ce komai ba sai dai Alhamdulillah. Tabbas idan mun gode zai ƙara mana. Ban taɓa haɗa makamancin taron nan ba, wannan ne na farko. Rashin masu tallafawa musamman daga ƴan Zariya duk da cewar ba ya gagare su ba ne. Rashin tallafawa ta ɓangarori daban-daban daga ɓangaren abokan tafiya da na kira su taimaka min.

Ba mu labarin Bookish Alchemy?

Bookish Alchemy, wanda a da yake Pen Warriors na samar da shi ne bayan na tashi da burin samun wajen da zan zauna na tattauna da marubuta, saboda rashin samun waje irin haka ya sa a maimakon na zauna ina ƙorafi sai na samar da shi. Mun fara a 2022 inda muka fara da gasar waƙen baka, (Poetry Competition). Bayan wani lokaci na fahimci yakamata a ce akwai hanyar da na samar wacce zan riƙa samun kuɗin shirya tarurruka duk irin waɗanda nake gani a wasu garuruwan, a haka na fara sayar da littattafai wanda yayi kusa da burikan da nake son cimma a Pen Warriors. Sannan kuma sai na ga ya fi dacewa da kulob ɗin mawaƙan baka. Shi ya sa sai na ƙirƙiro da Bookish Alchemy wanda na yi wa register da CAC domin ƙulla yarda tsakani na da kwastomomina da kuma samun tallafin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

A ƙarƙashin Bookish Alchemy, mun yi tarurruka mabambanta waɗanda suka sauya rayuwar matasa sama da 100.

Wacce gudunmawa ki ke bayarwa don farfaɗo da halayyar karatun littafi a tsakanin matasa?

Ta hanyar tarurrukan da nake shiryawa, kamar su tattaunawa da marubuta, tattaunawa akan littattafai a duk ƙarshen wata (book club), da sauran shirye-shirye da suka shafi harkar karatu da rubutu. 

Kin taɓa rubuta littafi ne? Wanne irin rubutu ne ya fi ɗaukar hankalinki?

 Ina dai da rubuce-rubucen da na yi da dama a ajiye. Har yanzu bana jin na kai matsayin da zan buga ko da ɗaya ne. Rubuce-rubuce ne na ƙirƙirarrun labarai. 

Wanne buri ki ke so ki cimma da taron da za a yi?

Ina burin ya zamana sanadiyyar farfaɗo da ɗabi’ar karatu da al’adunmu na koyo da koyarwa da ƙasar Zazzau tai shahara akai. Ina burin na samar wa marubuta masu tasowa dandali wanda duniya za ta ji muryoyinsu. 

Mene ne saƙonki na ƙarshe ga mahalarta da za su zo taron?

Da farko zan gode musu na ganin dacewar ziyartar Zariya don halartar taron duk da kasancewarsa kashi na farko.

Na biyu kuma, ina so su sani taro ne kashi na farko, duk wani kuskure da suka gani su yi haƙuri, in Sha Allah za mu gyara a karo na biyu. Abinda muka yi daidai kuma wannan tabbas daga Allah ne, kuma da ƙoƙarin masu bamu shawarwari ta bayan fage.

 To, muna godiya.

 Ni ma na gode.

By ukarofi