Gwamnan Niamey a Jamhuriyar Nijar Janar Abdu Haruna ya haramta wa masu gidajen mai sayar da mai cikin jarkoki ga kwastomomi.
Wannan mataki ya biyo bayan zargin da gwamnatin Niamey ta yi kan gidajen mai, cewa ƴan ta’adda na sayen mai domin zubawa a ababen hawansu don kai wa jama’a hari.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan Niamey Janar Abdu Haruna ya bada wannan umarni na hana sayarwa da ƴan bunburutu mai a faɗin jihar.
Janar Abdu ya ce ana sayar da mai da ya wuce hankali ga jama’a wanda a ƙarshe ƴan ta’adda ke amfani da shi wurin kashe mutane tare da kai hare-hare.
Don haka mun bada umarni ga kowanne gidan sayar da man fetur ya sanya kyamarorin tsaro
Tun shekaru kusan biyu da suka gabata ne dai aka haramta sayar da mai a galan da ya haura lita 50, sai dai da dama daga masu gidajen mai na bin dokar yayin da wasu ke karyata.
Ana ganin wannan mataki da aka ɗauka a Niamey da ke Jamhuriyar Nijar zai taimakawa hukumomi wurin bibiyar yadda ake hada-hadar mai a sassan jihar tare da tabbatar da tsaro.
