Jagororin NELFUND sun yi bayani kan badaƙalar karkatar da kuɗaɗen laminin ɗalibai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar gudanarwa ta Shirin bada Aron Kuɗin Karatu ga Ɗalibai (NELFUND), ta magantu game da zargin jagororin shirin da sauya aƙalar kuɗaɗen da gwamnati ta ware masu, biyo bayan rahotannin da ke cewa an tafka rashin gaskiya a yayin raba kuɗaɗen ga ɗaliban.

Hukumar Hana Rashawa da Makamantanta, ICPC, ta fara bincike game da batun zargin karkatar da kuɗaɗen laminin.

Haka kuma wani rahoto ya bayyana cewa, kimanin manyan makarantu 51 ne ake zargi da rage kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba da yin wasu haramtattun ayyuka kan harkokin shirin.

Saidai, NELFUND, ta bakin Darakta Manajansa, Akintunde Sawyerr, ya ce zarge-zarge da rahotannin suka yi ba su tabbata ba.

A yayin hira ta gidan telebijin na TVC a ranar Asabar, ya ce shirin ya raba Naira biliyan 54 ga makarantu 303 a faɗin Nijeriya.

Ya ce, an sanya biliyan N24 ne kai-tsaye a asusun ɗalibai, inda guda 293,000 suka amfana.

Ya kuma ce, sun samu bayanan da ke nuna cewa wasu makarantu sun riƙe kuɗaɗen karatun ɗalibai tare da wanda NELFUND ya tura masu, ya na mai cewa a wasu lokutan su kan buƙaci ɗaliban su yi ƙari akan asalin abinda ake biya, lamarin da ya fara haddasa zargin.

Har’ilayau daraktan ya ce, kimanin Naira biliyan 30 ne suka tura wa makarantu kai-tsaye da asusunsu.

Kazalika, ya yi kira ga dukkan wanda ya ke da wata ƙorafi da ya ziyarci shafinsa na yanar gizo domin faɗar matsalarsa, wanda ya ce a shirye suke su bada amsa.

By Babaji