Bauchi: Mahara sun kashe ƴan bijilante 11 a Alƙaleri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin ƴan bijilante 11 ne suka rasa rayukansu a ƙauyen Mansur dake Gundumar Gwana a Ƙaramar Hukumar Alƙalerin Jihar Bauchi, biyo bayan wani hari da ƴan ta’adda suka kai wa yankin.

Mazauna suna shaida wa manema labarai cewa, maharan sun kuma yi awon-gaba da wasu dabbobi masu tarin yawa.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin mai suna Abubakar Bello, ya ce waɗanda suka rasu a yayin harin, ƴan bijilante ne da ke aikin bada kariya ga ƴan ƙauyen.

Ya ce, maharan sun kai farmaki ne ga ƴan bijilanten a lokacin da suke sintiri a ƙauyukan Mansur, Digare da Yalo inda galibi manoma ne a yankunan waɗanda ke kusa da yankin mai a ƙaramar hukumar.

Bellon ya ƙara da cewa, lamarin ya haddasa zaman ɗar-ɗar acikin al’ummar a yayin da suke shirin fara shuka a gonakinsu.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Wakil a wata sanarwa, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:40 na asubahin ranar Lahadi wanda ya kuma yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ƴan ta’addar.

By Babaji