Daga HUKUMAR SHARI’A TA KANO
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, bayan zarge-zargen da ka yi akan gidan gyaran hali da tarbiyya na Gwauron Dutse na cewar ana lalata da wasu ɗaurarru a gidan! To alhamdulillah wannan hukumar ta yi duk abinda ya dace wajen bincike akan wannan zargin da ka yi, mun gayyato limaman wannan gida tun da ka ce kai na ibinsu ne, sannan mun gayyato Kakakin hukumar shi ma ya amsa mana tambayoyin mu, sannan bamu yi ƙasa a guiwa ba wajen haɗa tawaga ta musamman muka shiga gidan domin ƙara bincika zargin da ka ke yi, amma cikin ikon Allah ma ba mu sami wani abu kusa da wanda ka yi zargi a kai ba.
Bayan wannan ma mun sake bincika rijistar gidan na farkon zamanka da ranar da kace ka fita 29 Afrilu babu mai irin wannan sunan gaskiya, har ɗakin da ka faɗa mun shiga mun yi binciken ƙwaƙwaf amma babu wannan zargi, shi kansa shugaban wannan gidan shima ya ce a bayan liman ya ke zama a masallacin tun da ya zo wannan gidan amma bai san ka ba!
Don haka wannan hukumar Shari’a take gayyatar ka domin kazo kayi mana cikakken bayani akan wannan zargin ta yadda za mu gano wannan zargin naka, domin a gaskiya mu bamu ga komai ba akan wannan maganganun naka, an bamu wayarka mun kira mun kasa samun ka, don haka muke bada wannan saƙo gare shi ko wanda ya san shi ya sanar da shi ya zo hukumar shari’a ta Jihar Kano dake lamba ɗaya, titin Abdullahi Bayero, Kano.
Sa Hannu;
Musa Ahmad Durumin Iya,
Muƙaddashin daraktan wayar da kai,
Hukumar Shari’a ta Kano
