Mun faɗawa shugaban ƙasa abu uku da ke damun Jihar Katsina – Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo ziyarar aiki Katsina mun zauna da shi mu faɗa masa abu uku da ke damun jihar.

“Mun faɗa masa cewa muna da matsalar tsaro da kuma rashin kammala tashan wutan lantarki na Lambar Rimi(Wind Mill) da kuma ayyukan da aka bada a filin tashi da sauka na Umaru Musa Yar’adua da ba a kammala ba.

Gwamnan na maida martani ne akan kalamai da wasu fitattun yan jihar suka yi akan wani allo da aka kafa ɗauke da rubutun”KATSINA BA KORAFI” da wasu ke zargi da sanin gwamnan aka kafa lokacin da shugaban ƙasa ya kawo ziyara a jihar.

Shi dai wannan allo ya sha suka daga mutane a ciki da wajen jihar da akai ta yaɗawa a kafafen sadarwa na yanan gizo.

Duk da gwamnan bai yi bayanin abinda waɗannan mutane suka faɗa masa ba ,yayi godiya a gare su sai dai shawara ce su da su rinƙa bincike maimakon yanke hukuncin abin da basu da masaniya a kai.

“Ba ni nasa a kafa wannan allo ba,ban san an kafa ba kuma bada yawu na aka kafa ba, ban san wanda ya kafa ba”inji Dikko Raɗɗa.

Ya jawo hankalin irin waɗannan mutane masu faɗa aji da su rinƙa tuntuɓar sa idan suka ga anyi kuskure domin a gyara” matsayi na na shugaba ban wuce inyi kuskure ba domin nima ɗan Adam ne kamar kowa Dikko yace.

By ukarofi