
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kaddamar da jigilar Mahajjata na farko daga Nijeriya zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji na Shekarar 2025, inda ya bukaci da su tabbatar da halayensu na gari a lokacin zamansu a ƙasa mai tsarki, yana mai nuna ƙima da darajar da Nijeriya ke da shi.
An gudanar da bikin tashin maniyatan ne a Filin jirgin sama na Sam Mbakwe dake Owerri a Jihar Imo a karon farko, inda kimanin maniyatan Najeriya 64,188 ne suka yi rajistar aikin hajjin na bana.
Ya kuma bukaci jami’an kula da maniyyatan da su rike aikinsu a matsayin wani aiki da Allah ya dora musu ta hanyar tabbatar da cewa kowane mahajjaci ya dawo Gida Najeriya cikin farin ciki ba tare da wani korafi ba
Shettima ya kuma yaba wa Gwamna Hope Uzodimma kan inganta hadin kai da goyan baya a tsakanin addinai,ta hanyar amincewa da bikin kaddamar da jirgin farko a jihar sa,inda yace alama ce dake nuna cewa Al’umar Najeriya tana zaune cikin hadinkai
Kazalika Shettima ya kuma isar da sakon fatan alherin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Mahajjatan,yana mai cewa Shugaba Tinubu ya samar da dukkanin abubuwan jindadin su domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2025,inda yace yana daga cikin alkawuran da Gwamnatin Tarayya ta daukar wa jama’a na kare rayukan su da kuma tallafa musu a kowane fanni na rayuwa
Shettima ya kuma mika sakon godiya ga shugabancin Hukumar Kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON)tare da masu ruwa da tsaki,da suka yi aiki tukuru wajen tsara aikin Hajjin na 2025 da kuma tabbatar da nasarar gudanar da ayyukan sa
A nasa bangaren Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci na Najeriya (NSCIA), Alhaji Mohammad Sa’ad Abubakar III, ya yabawa Gwamnan Jihar Imo kan kokarinsa na inganta zaman lafiya a tsakanin addinai a jihar.



