Matashi ya sassara mahaifinsa da adda har lahira a Jigawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani matashi ɗan shekarar 20 ya faɗa hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa.

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda.

Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafaɗarsa da wuya da ƙirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin 5 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Bakin Kasuwa, da ke ƙaramar Hukumar Gwaram.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Jigawa, AT Abdullahi, ya ba da umarnin cewa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Dutse su karɓi ke cin domin don gudanar da bincike mai zurfi, wanda bayan nan za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.

Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kama wanda ake zargin tare da ba da tabbacin cewa za a yi adalci kuma za a bayar da ƙarin bayani a nan gaba.

By ukarofi