Daga SALIHU ISHAQ MAKERA Bauchi
Hukumar Zaɓe ta Jihar Bauchi (BASIEC), za ta gudanar da zaɓen cike gurbi a ƙaramar hukumar Shira da ke jihar don zaɓen shugaban ƙaramar hukumar da mataimakinsa a ranar 24 ga watan Mayu, 2025.
Shugaban hukumar BASIEC Alhaji Ahmed Makama ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Bauchi a yammacin ranar Alhamis da ta gabata.
Alhaji Ahmed Makama ya bayyana cewa an samu gurbin shugaban ƙaramar hukumar da mataimakinsa ne saboda kansilolinsu sun tsige su a kwanakin baya.
Hukumar ta ce bisa dokar zaɓe ta 2008 za a fara kamfen na neman muƙaman biyu tun daga ranar ranar Alhamis 8 ga Mayun nan.
Shugaban ya ce duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukumar zai yanki fom a kan Naira miliyan ɗaya mataimakin shugaba kuma a kan Naira 500,000.
Hukumar ta ce za ta zauna da jami’yyun siyasa da shugabannin hukumomin taro da masu ruwa-da-tsaki kan zaɓen a wannan mako a ofishinta na Shira.
Ya ce, yayin da jam’iyyu za su gudanar da zaɓuɓɓukan fitar da ‘yan takara, hukumar a nata ɓangaren za ta horar da malaman zaɓe da masu duba yadda za a gudanar da zaɓen da sauran shirye-shiryen zaɓen.
Shugaban ya ce za a raba kayan yin zaɓe Kuma a ranar za a ana gobe zaɓen kuma a kawo ƙarshen kamfe ranar 23 ga Mayu washe gari 24 ga watan a gudanar da zaɓen.
Alhaji Ahmed Makama ya ce an shirya ingantaccen zaɓe da kowa zai gamsu.
Alhaji Ahmed ya buƙaci al’ummar yankin da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa-da-tsaki su taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin nasara da kwanciyar hankali.
