Borno: Gwamna Zulum ya haramta sayar da fetur a Karamar Hukumar Bama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani rahoto daga Maidugurin jihar Borno ya ce, Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci a hana sayar da man fetur a gidajen man dake Karamar Hukumar Bama ciki har da na cikin garin Bama da Banki.

A wata takarda da mai taimaka masa kan harkar labarai, Dauda Iliya ya fitar, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin ne a kokarinta na dakile ayyukan ta’addanci.

Ya ce, lamarin ya biyo bayan shawarwari da gwamnatin ta yi da hukumomin tsar da nufin warware kalubalen tsaro a jihar.

Gwamnan ya kuma yi gargadin cewa, duk wanda aka samu ya bijire wa dokar, zai fuskanci fushin doka.

Kazalika, ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da kokarin dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar, ya na mai kira ga al’umma da su bada hadin-kai wajen yaki da ta’addaci a sassan jihar.

By Babaji