Disney zai fitar da ‘Descendants’ na biyar

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Kamfanin fina-finai na Disney ya tabbatar da cewa, fim na biyar cikin shahararren jerin Descendants zai fito da suna ‘Wicked Wonderland’ a shekarar 2026. Wannan sabon fim zai bayyana a tashar Disney Channel da kuma dandamalin Disney+, inda za a ci gaba da labarin ‘ya’yan manyan azzaluman da suka fito daga tatsuniyoyin Disney.

 A cikin wannan gawurtaccen fim mai fitowa za a ga fitattun jarumai da suka yi fice a fim ɗin da suka gabata, ciki har da:

Brandy Norwood a matsayin Cinderella, Paolo Montalban a matsayin Sarki Charming, Rita Ora a matsayin Sarauniyar Zuciya (ƙueen of Hearts), Melanie Paɗson a matsayin Uwa mai sihiri (Fairy Godmother), Kylie Cantrall a matsayin Red, ‘yar Sarauniyar Zuciya, Malia Baker a matsayin Chloe, ‘yar Cinderella da Sarki Charming.

Haɗuwar Brandy da Montalban ta sake ɗaga hankalin masu kallo, domin sun dawo da jaruman fim ɗin Cinderella da suka taka rawa tun shekarar 1997.

A ɓangare guda za a ga sababbin fuskoki a ɓangaren jarumai, irin su: Pink (ƴar ƙaramar Sarauniyar Zuciya), Maɗ Hatter (ɗan maddoɗ Hatter), Luis Madrigal (ɗan Luisa Madrigal), Hazel Hook (ƴar Captain Hook), Robbie (ɗan Robin Hood), Feliɗ (ɗan Dr. Facilier), Sƙueaky da Sƙuirmy, (ƴan tagwayen Mr. Smee) da sauransu. 

Fm ɗin zai cigaba da labarin Descendants: The Rise of Red, inda Red da Chloe suka yi amfani da sihiri su koma baya cikin lokaci. Wannan tafiya ta kawo sauye-sauye a tarihin duniya, kuma yanzu suna fuskantar matsalolin da suka haifar. A yayin da gasar Kingdom Cup ke tafe, Red da Chloe dole ne su fuskanci sakamakon ayyukansu tare da neman mafita.

Fim ɗin zai kasance cike da kiɗa, ban dariya, sihiri da ƙalubale — abin da zai ɗauki hankalin yara da manya.

An fara ɗaukar fim ɗin a farkon shekarar 2025 a ɓancouɓer, Canada.

By ukarofi