Daga AISHA ASAS
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta gayyaci fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Iyabo Ojo, da kuma shahararren jarumin barkwanci Ayo Makun (AY) domin yi musu tambayoyi kan yadda aka watsa takardun Naira a fili yayin wasu bukukuwa da suka halarta — abin da ya saɓa wa dokar Najeriya.
Iyabo Ojo ta bayyana cewa, EFCC ta gayyace ta bayan bikin ɗiyarta, Priscilla, inda baƙi suka watsa Naira da kuɗaɗen ƙasashen waje. Ta ce tana ƙasar Ingila lokacin gayyatar ta zo, kuma da ta dawo a ranar 5 ga Mayu, 2025, ta halarci ofishin hukumar kamar yadda aka buƙata.
A cewarta, jami’an EFCC sun nuna mata bidiyon bikin sannan suka tambaye ta kan asalinta da sana’ar da take yi. Ta ce a ra’ayinta, tana tunanin mutilation (lalata Naira) kaɗai ne laifi, ba watsa kuɗi ba. Sai dai hukumar ta tabbatar mata cewa duk wani nau’in watsa kuɗi — ko Naira ne ko kuɗin waje — laifi ne a Najeriya.
Iyabo ta ce, an sako ta ranan da ta je, tare da lauyanta, sannan ta shawarci jama’a su kauce wa irin wannan aiki domin kauce wa faɗa wa hannun hukumar.
Shi ma a nasa ɓangaren jarumin barkwanci AY Makun ya tabbatar da cewa EFCC ta gayyace shi a ranar 5 ga Mayu, 2025, kan wani taro da aka watsa kuɗi a fili. Ya ce ya gode wa hukumar bisa yadda ta gudanar da bincike cikin girmamawa, kuma ba a samo wata alaƙar kuɗin da wani aikin haram ba.
AY ya ce, ya ɗauki darasi, kuma zai fara amfani da kafafen sadarwarsa wajen faɗakar da jama’a kan yadda za su mutunta kuɗun Najeriya da kuma bin doka.
Dokar Sashe na 21 a cikin CBN Act, 2007 ta bayyana cewa, watsa kudi, taka su ko rawa a kai, da kuma duk wani amfani da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba na iya jawo hukuncin zaman gidan yari na aƙalla wata shida ko tara ta aƙalla Naira 50,000 ko duka biyun.
Wannan mataki na EFCC wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na daƙile raini da cin zarafin kuɗin ƙasar, domin kare darajar su a idanun duniya da ‘yan ƙasa.
