Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wani ɗan jarida ya yi wa wani tsohon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ɗan ƙasar Netherlands Clemens Westerhof tambaya a lokacin da ya gama kwatiragin aikinsa cewa a ƙasar nan, ‘Ko me zai riƙa tunawa da shi game da Nijeriya bayan ya koma gida?’ Sai Clemens Westerhof ya kada baki ya ce, ‘Ba ƙorafi!’
Yayin da ɗan jaridar ya nemi ƙarin bayani a wajen sa, sai tsohon Kocin ya ce masa, a duk lokacin da za ka haɗu da ɗan Nijeriya ka tambaye shi, ‘Yaya ka ke?’ ‘Ko yaya ake ciki?’ Amsar da zai fara baka shi ne, ‘Ba ƙorafi!’
Don haka Westerhof ya ce musamman ya sa an buga masa waɗannan kalmomi guda biyu masu muhimmanci a wajen ɗan Nijeriya, zai je ya buga a ɗakinsa don ya riƙa tunawa da su. Kamar abin dariya ko? Ko kuma dai abin takaici?
Mutum zai ji maganar kamar gatse a ce ɗan Nijeriya ba shi da damuwa ko kuma bai san ciwon kansa ba. Wannan maganar fa an yi ta ne a shekarar 1994, lokacin da matsalolin ‘yan Nijeriya ba su kai abin da ake fuskanta a halin yanzu ba. Lokacin da abinci da kayan masarufi ba su fi ƙarfin talaka ba. Sannan babu matsalar tsaro da a yanzu take addabar ƙasar nan, in ban da ta fashi da makami, da batun dambarwar siyasar zaɓen Abiola da ta dabaibaye ƙasar. Yayin da zazzafar adawa tsakanin ɓangaren Kudanci da Arewaci ke cigaba da haifar ɓaraka a tsakanin ’yan ƙasa. A lokacin za a iya cewa ’yan Nijeriya na rayuwa cikin kwanciyar hankali, don haka babu laifi idan sun ce ba su da ƙorafi.
Amma a yanzu da matsaloli suka dabaibaye ko ina a ƙasar nan, kama daga matsalar tsaro, masu garkuwa da mutane, lalacewar tattalin arziƙi, yunwa, gurɓacewar muhalli, da ƙaruwar rashin yarda a tsakanin ’yan ƙasa, akwai ganganci a ji wani ɗan Nijeriya yana ikirarin cewa, ‘Babu ƙorafi!’
Na san ya zuwa yanzu mai karatu zai fahimci inda rubutuna ya karkata. Wato ina so na yi tsokaci ne game da dambarwar da ta biyo bayan bikin ’yar Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa, wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu halarta, tare da wasu manyan ’yan siyasar ƙasar nan. Game da allunan kan hanya da aka kakkafe ɗauke da hotunan Shugaban ƙasa da na Gwamna, ana yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu murna da zuwa Katsina, waɗanda suka ja hankalin ’yan Nijeriya da dama. Babu ma kamar rubutun da aka yi a jikin allunan da ke cewa, ‘Katsina ba ƙorafi!’
An yi ta bayyana rashin dacewa da cancantar yin wannan rubutu a daidai lokacin da Jihar Katsina ke tsakiyar fuskantar hare-haren ’yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka. Suna ta’addancin su kan mutane da gayya, a sace na sacewa, a kashe na kashewa, a tarwatsa duk ƙauyen da ya nemi yin turjiya, ko rashin ba da haɗin kai.
Kodayake Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta da hannunta cikin kafa waɗannan allunan ko kalmomin da aka yi amfani da su, da suka tunzura jama’a, amma za a iya cewa, ba baƙon abu ba ne a wajen ’yan Nijeriya. Mutum na cikin matsala tsundum, amma da ka tambaye shi za ka ji ya ce maka ba matsala. Mai yiwuwa kuma za a iya cewa, tawakkali ne da miƙa al’amura ga Allah.
Amma dai ya kamata a ce kawo yanzu kan ɗan Nijeriya ya waye, ya san inda yake masa ciwo, musamman ma ɗan Arewa. Jariri na goye ne kaɗai za a iya cewa bai san halin da ƙasar nan ke ciki ba. Ko shi ɗin ma na san ba ya samun ruwan nono isasshe, musamman ga matan Katsinawa da ke zaune a lungunan da ake fuskantar tsananin hare-hare.
A gaskiya ko ma wane ne ya ɗauki nauyin buga waɗannan fostoci bai yi wa kansa adalci ba, kuma bai yi wa mutane Jihar Katsina adalci ba. Saboda sanin kowanne ɗan Nijeriya ne Katsina na daga cikin jihohin ƙasar nan da ke fama da matsanancin ƙalubalen tsaro, don haka a fito da wannan maganar ma rashin tunani ne, da rashin sanin lissafin siyasa.
Kuma nasan duk da yake ba lallai shugaban ƙasa ya ga wannan rubutun ba, ko kuma ya iya fahimtar me ake nufi a jiki ba, sai dai daga baya ya karanta a jaridu. Amma shi ma da kansa ya san Jihar Katsina na da matsala. Don ko a cikin jawabin da ya gabatar ya sake nanata ƙoƙarin da gwamnatin tarayya take yi na shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihar.
A maimakon wannan rubutu na rashin sanin ciwon kai, da wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki, gayyato jama’a ya yi su fito su tarbi shugaban ƙasa a titunan da aka ware zai bi zuwa wajen taro, su riƙe kwalaye masu ɗauke da bayanan halin da al’ummar jihar ke ciki, suna neman ɗaukin shugaban ƙasa da Gwamnatin Tarayya. Yayin da suke ɗaga tutar Nijeriya da hotunan shugaban ƙasa da na Gwamna. Mai yiwuwa in da an yi haka za a ce lallai an yi ƙoƙari wajen jan hankalin gwamnati da ƙara kai kukan jama’ar Katsina ga shugaban ƙasa. Kuma wannan ba zai ɓata siyasar duk mai yin hakan ba, don an san ya yi haka ne saboda kishin al’ummar sa ta Katsina. Jama’ar Katsina na da ’yancin yin hakan, kuma hakkin gwamnati ne ta ba su cikakken tsaro, saboda tsari ake bi na dimukraɗiyya.
Amma rubuta, ‘Katsina Ba ƙorafi’, kuskure ne mai girma, da rashin sanin ciwon kai. An ɓarar da damar da aka samu wanda jama’a za su kai kukansu kai tsaye ga shugaban ƙasa, ba tare da hayaniya ko yamutsi ba. Kuma babu shakka ’yan jaridu na gida da na waje za su ƙara kambama abin ta yadda saƙon zai kai kunnen shugaban ƙasa, kamar yadda wannan abin da aka yi shi ma ya ja wa jama’ar Katsina tofin Allah wadai.
Ya kamata ‘yan Arewa da ‘yan siyasar mu su riƙa sanin ciwon kansu da neman hanyoyin magance matsalolin su ta inda ya dace. Sarayar da haƙƙoƙinmu da muke yi saboda kwaɗayi da neman gindin zama ba zai fisshe mu da komai ba, sai zagi da wulaƙanci. Shi ya sa ’yan uwanmu da ke Kudu suka fi mu morar gwamnati da shan romon dimukraɗiyya, saboda mu muna nuna ba mu san matsalar mu da ta ’yan uwanmu ba, mulki kawai muka sani.
Gaskiya ya kamata mu yi wa kan mu faɗa, wannan shiriritar da muke yi da sunan gyara siyasa, ƙara kashe mu yake yi in ba mu sani ba. Allah Ya ganar da mu, da shugabannin mu!
