Majalisar Dokokin Katsina ta amince da ƙudirin dokar kafa cibiyoyin sulhu a tsakanin al’umma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Shugaban kwamitin kula da harkokin shari’a na majalisar Hon Lawal Abdu Ƙanƙara ya karanta rahoton da kwamitin da aka kafa na jin ra’ayin mutane game da dokar.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci majalisar da ta samar da wannan doka,bisa la’akari da yawan jama’a a kotuna inji shugaban kwamitin.

A cewar sa ganin yadda da yawa laifuffukan ba sai an je kotu ba,gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci majalisar ta samar da ƙudirin dokar.

Hon Lawal Abdu ya bayyana cewa da zarar gwamna ya sanya hannu a dokar bayan majalisar ta miƙa masa to cibiyoyin zasu rage cunkoso na jama’a a kotuna.

Haka kuma majalisar ta amince da dokokin haraji da na ma’aikatan majalisar dokokin jihar.

Duk dai a wannan zama ƙarƙashin kakakin majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ɗan majalisar ƙaramar hukumar Katsina Hon Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar da ƙudirin buƙatar farfaɗo da cibiyoyin gyara da canza tunanin masu harkar shaye shaye a jihar.

Albaba ya buƙaci a sanya kayayyakin koyon sana’o’i kamar yadda tsarin wuraren yake, a cewar sa hakan zai kawar da hankalinsu daga shaye shaye da kuma koya masu sana’o’in da zasu zama masu dogara da kai.

By ukarofi