Kano: DSS ta kama ƴan bindiga biyar bisa zargin kashe ƴar shekara daya bayan karbar kudin fansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa, jami’an ƴan sandan farin kaya, DSS, sun yi nasarar kama wasu mutane biyar bisa zargin su da yin garkuwa da yar shekara daya mai suna Sakina Mamuda, inda suka kashe ta bayan sun karbi kudin fansa a hannun iyayenta.

Lamarin ya auku ne a Kauyen Duhum Bake dake Karamar Hukumar Gwarzo a jihar.

An yi zargin cewa waɗanda suka sace ta su ma ƴan kauyen ne, waɗanda bayan kashe ta ne sai suka jefa ta acikin wata rijiya da aka daina amfani da ita.

Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa a wata takarda, ya koka game da aukuwar lamarin wanda ya jefa al’umma cikin zaman dar-dar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana al’amarin a matsayin abin rashin hankali da ya girigza jihar, ya na mai yaba wa DSS bisa hobbasa da ta yi cikin kankanin lokaci.

Ya kuma ce, lallai sai an hukunta waɗanda aka samu da hannu a laifin domin hakan ya zama izina ga masu tunanin aikata irinlaifin.

Waɗanda aka kama sun hada da Zailani Rabiu, Hafizu Yusuf, Abubakar Abdulkareem, Umar Lawan, da kuma Amadu Salisu, inda aka tsare su bisa tuhumar aikata laifukan makirci, garkuwa da mutane gami da kisa.

A yayin hira da manema labarai a Gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen habaka tsaro a baki daya sassan jihar.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da kasancewa masu kula da sanya ido kan ababen da ke kai-kawo acikinsu da ruwaito wa hukuma dukkan wani abin zargi.

By Babaji