Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Samira Sani ƴar asalin garin Kano ce da ta shigo Masanartar Kannywood a shekarar 2022, a tattaunarta da wakilinmu a Kano Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ƴan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim:
MANHAJA:Za mu so ki gabatar da kanki?
SAMIRA: Sunana Samira Sani, jaruma a masanartar fim ta Kannywood.
Mene ne tarihinki a taƙaice?
To ni ƴar asalin garin Kano ce, an haife ni a garin Dakatsalle da ke ƙaramar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano, na yi primary da secondary duk a Dakatsalle, bayan gama secondary sai akai min aure, daga baya Allah ya kawo ni cikin birnin Kano.
Kenan kin taɓa yin aure?
Eh na taɓa yin aure, kuma ina da ƴaya guda uku.
Ta yaya kika samu kanki a Kannywood?
Ta sanadiyyar wata ƙawata, wacce take yar fim ce tana gayyata ta muna zuwa ‘location’ a hankali a hankali, yan Kannywood suka sanni, ni ma na san mutane.
A wacce shekara kika shiga Kannywood?
Na shiga ne a shekara 2022, shekaru uku kenan, amma ban fara ‘acting’ ba sai a shekarar 2023.
Me ya baki sha’awa kika shiga Kannywood?
A da gaskiya ba na sha’awar Kannywood.
Saboda me ?
Saboda yadda ake zagin ƴan fim, ana cewa ƴan iska ne, to sakamakon na shiga cikinsu na ga irin yadda suke da mu’amala mai kyau, suna son junansu, domin idan na je ana ɗaukar fim za ka ga ana wasa da dariya, har sai ka ji ba ka son rabuwa da su.
To a haka sai na fuskanci abinda ake faɗa akan ƴan fim ba gaskiya ba ne, wasu ne suke masa kallo a baibai, to daga nan sai na ji ina sha’awar abin to sai na fahimtar da iyaye na da ƴan uwa na, to a haka na shiga Kannywood, inda na fara a hannun Darakta Mujahid M. Soja.
To kenan sai da kika fara mu’amala da ƴan Kannywood sannan kika fara fim da su haka ne?
Kwarai kuwa, sai da na fara mu’amala da su sannan na shiga Kannywood, saboda a gaskiya ada ina dari-dari da shiga fim ina gudun kar a ce mini yar iska to amma da na yi mu’amala da su sai na fahimcesu, kuma na ga abinda ake yi a waje ba a yinsa a fim, domin ina mu’amala da yan fim ina yi da waɗanda ba ƴan fim ba, shekara biyu ina mu’amala da ƴan fim sannan na fara.
To da wane fim kika fara?
Na fara da wata waƙa ne mai suna Ladidi mai Koko da Sosai, wacce muka yi da dan ƴarbawa da kamal Aboki (marigayi) da Adam Dorayi , a ɓangaren fim kuwa na fara da ‘Ƴar Tiktok’ na Darakta Mujahid M. Soja.
Ya zuwa yanzu finafinai nawa ne kika yi?
Za su kai takwas zuwa tara sun haɗa da: ‘ƴan Tiktok’, ‘Soyayya ɗaya’, ‘Buri’, ‘Niniya’, ‘Umarni’ da kuma ‘Jikokin Maigari’ da sauransu.
