Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Nasir el-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ba zai iya jan ragamar jam’iyyar adawa ba.
A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Galadima ya yi iƙirarin cewa el-Rufai ya kasance mai riƙe wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ragamar jam’iyyar SDP kafin ya shigo.
“Ina da yakinin cewa tunani na zai yi daidai saboda El-Rufai ba zai iya jagorantar jam’iyyar adawa ba, kawai alhali ne ke kama shi,” in ji shi.
“Ya saba shiga jam’iyyar bayan an gama gina ta, amma yanzu da yake ƙoƙarin gina wata tun daga tushe, zai ga yadda siyasa ke da wahala.
Jigon na NNPP ya ba da shawarar cewa aikin el-Rufai a cikin SDP na wucin gadi ne, kuma ya zama mataimaki ga Atiku, wanda ake sa ran zai karɓe jam’iyyar.
