
Daga BELLO A. BABAJI
Kotun Adalci ta ECOWAS, ta yanke hukuncin bada Naira miliyan 20 a matsayin kuďin dameji ga Mista Moses Abiodun, bayan tsare shi da aka yi na tsawon shekaru 16 ba tare da an gurfanar da shi ba.
Mutumin ya maka Gwamnatin Tarayya ne a Kotun bisa zargin tauye hakki na ƴancin walwala da gurfanarwa da aka yi masa na tsawon lokacin.
Mista Abiodun, ta hannun lauyansa, Chigozie Uzodinma, ya ce jami’ai na musamman kan lamuran fashi da makami (SARS), sun kama shi ne a watan Nuwamban 2008, inda suka tsare shi na tsawon watanni da dama.
Ya ce, a ranar 23 ga watan Maris, 2009 ne wata kotun shari’a a Legas ta tura shi gidan yari bisa laifin makirci da fashi da makami, inda tun daga nan ba a sake gurfanar da shi ba.
Bayan fitowarsa ne, ya yi ikirarin tauye masa hakki da hana a kare masa mutuncinsa sakamakon kunci da aka sanya masa da nuna rashin tausayi a gare shi, duk da cewa kundin dokar ƴancin al’umma ta Afirka, wato ‘African Charter on Human and People’s Rights and Other International Human Rights’ ta yi hani akan haka, wadda Nijeriya na ďaya daga cikin kasashen da ke amfani da ita.
Duk da cewa wadda aka shigar da kara ta musanta sanin shigar cibiyar SARS a batun da kalubalantar sahihancin takardar izinin tsarewa da mai karar ya gabatar, kotun ta tabbatar da su tare da yanke hukuncin biyan Abiodun kudaden bisa damejin da aka yi masa.
