JAMB: Majalisar Wakilai za ta binciki tsaikon da aka samu a jarrabawar 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta umarci a gudanar da bincike game da tsaikon da ya haifar da matsaloli a jarrabawar UTME ta shekarar 2025, wanda Hukumar JAMB ta gudanar.

Majalisar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa cibiyoyin rubuta jarrabawar (CBTs) a baki ďaya kananan hukumomin Nijeriya 774 don saukake hanyoyin jarrabawar ga ďalibai.

A ranar Alhamis ne majalisar ta cimma matsayar a yayin zamanta, bayan da Hon. Adewale Adebayo (Osun) ya gabatar da kudirin.

A ranar 9 ga watan Mayu ne JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar, wanda ya nuna an samu gagarumar faďuwa, inda Rajistiran hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce an samu tsaiko ne wajen sadarwa wanda ya shafi kimanin ďalibai 379,997.

Hon. Adebayo ya koka da faruwar lamarin, inda ya ce ďaliban da iyalansu sun jure wa tafiya na dogon zango zuwa wuraren da aka tura su amma hakan bai sa sun yi nasara ba, ya na mai kira da a gudanar da bincike don gano hakikanin abinda ya sabbaba hakan.

By Babaji