
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce sojoji da sauran hukumomin tsaro suna aiki tukuru wajen kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Gabas sakamakon sake farfaďowar ayyukan tada kayar baya a shiyyar.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ranar Alhamis.
Ya ce, duk da cewa shi da ministan tsaro da sauran jagororin tsaro sun halarci Borno makonni kaďan da suka gabata, hakan bai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake dawowa da nufin duba matakin hare-haren da kokarin kawo karshen su.
Ya kuma ce, Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu tana aiki haikan wajen ganin ta samar da zaman lafiya mai ďorewa a dukkan sassan Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, a lokacin da ya kai ziyara ƙasar Rasha, sun tattauna da masu-ruwa-da-tsaki inda suka amince da su haďa hannu da ƙasar wajen yaki da ta’addaci a Nijeriya.
Kazalika, Babban Hafsan ya gana da jagororin tsaro da ziyartar barikin Giwa da aka samu tarwatsewar ababen fashewa a wajen ajiyar kayan yakin sojoji, kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN ya ruwaito.
