Nijeriya ta tabbatar da kammala biyan IMF bashin Covid-19 na dala biliyan 3.4

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da kammala biyan bashin da ta karɓo daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF na dala biliyan 3.4 domin yaƙi da annobar Covid-19 a ƙasar.

Ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ne ya tabbatar da haka ranar Litinin, a lokacin jawabin da ya yi wa manema labarai, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa a fadar gwamnatin ƙasar.

”Za mu iya tabbatar da cewa Nijeriya ta fice daga ƙangin bashin IMF, kuma abin da hakan ke nufi shi ne mun kammala biyan bashin da Asusun ke bin ƙasarmu”, kamar yadda Ministan ya bayyana.

A makon da ya gabata ne labarin kammala biyan bashin ya bayyana bayan da Asusun ya fitar da wani rahoto na jerin ƙasashen da yake bin su bashi.

To sai dai tun daga lokacin Nijeriya ba ta sanar da haka a hukumance ba.

Masana sun ce matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da nasarar ƙasar a fannin tsare-tsaren tattalin arzikinta.

By ukarofi