Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kashe Naira biliyan shida cikin shekara guda wajen gina da gyaran makarantun firamare guda 700 a faɗin jihar.
Shugaban hukumar ilimi na bai ɗaya SUBEB a jihar Katsina Dr Kabir Magaji ya sanar da haka a lokacin da yake hira da manema labarai a ofishin sa.
Dr Kabir ya bayyana wannan kuɗi kaso da gwamnatin jihar ta ke ba hukumar da ita ma hukumar UBEC kason da take ba jihohi.
Ya ce a wannan shekara ma gwamna Dikko Raɗɗa ya ruɓanya kaso kuɗin zuwa Naira biliyan 13, da hakan ya nuna irin mahimmancin da gwamnan ya baiwa ilimi musamman ilimin firamare a jihar.
Kuma Dikko Raɗɗa ne gwamna na farko da ya amince a sakamma hukumar ilimin kason gwamnatin jihar na watanni shida na farko wannan shekara 2025.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa wannan ƙarin kuɗi da hukumar ta samu ,zai bata damar gina da gyaran wasu makarantun fiye da 1000 a faɗin jihar.
Ya ce ita kan ta hukumar ta gina wasu ƙarin makarantu guda ashirin a jihar.
Hukumar ta kuma gina gidaje guda ashirin ga malaman da ke koyarwa a ƙauyukan da ke fama da matsalar rashin kyawun hanyoyi da rashin matsuguni a makarantun karkara Dr Kabir ya ce.
“Gwamna Dikko Raɗɗa ya raba wa waɗannan Babura guda 70 ga waɗannan malamai da ke koyarwa a karkara domin ƙara masu ƙarfin gwiwa.
Ya bayyana cewa hukumar UBEC ta ƙasa ta biya su kason ta na Naira miliyan 500 domin ba malaman jihar horo akan fanni daban daban da zai taimaka ma su wajen harkokin malantar su.
Dr Kabir ya bayyana cewa jihar Katsina na da yawan malaman firamare dubu 28 da a cikin su malamai dubu 18 hukumar ta basu horo akan darussan ilimin addinin musulunci, lissafi, harshen Larabci, kimiyya da sauran su.
Akan matsalar tsaro kuwa da yasa aka rufe makarantun firamare a wasu ƙananan hukumomi kuwa, shugaban hukumar ya sanar da cewa yanzu haka shugabannin ilimi a ƙananan hukumomi bakwai sun rubuta wa hukumar suna neman izinin buɗe makarantun da ke rufe.
