Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta yi kira ga jami’an tsaro a jihar da su kamo shugabar matan jam’iyyar PDP na jihar, Hajiya Rabi Madawaki bisa barazanar da ta yi wa masu zaɓe gabanin zaɓen 2027 a jihar.
Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a yammacin yau mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jihar Yusuf Idris.
Jam’iyyar ta zargi shugabar matan Hajiya Rabi Madawaki da bayyana barazanar da ta yi wa masu zaɓe a zaɓen 2027 cewa duk wani mai zaɓe da ya ƙi zaɓen PDP a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal a wa’adinsa na biyu to zasu lakaɗa mashi duka ko ma a kasheshi a zaɓen 2027.
“Shugabar matan Hajiya Rabi tayi furucin ne da harshen Hausa a wani taro da aka yi a Gusau a ranar Juma’a 16/5/2025 wanda aka fassara da cewa, ‘Duk wanda bai zaɓi Dauda ba, za mu raunata shi, mu doke shi, mu kashe shi,’ (zamu ci ubanshi zamu yi mashi duka), kuma ta faɗi waɗannan kalamai ne don aikewa da saƙonta ga jama’ar jihar. ” A cewar APC.
“APC a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a jihar ba za ta tsorata da duk wata barazana daga gwamnatin PDP ba a Zamfara, kuma su sani cewa dole ne muradin al’umma ya yi nasara”.
“Shugabar mata ta PDP ta jihar, Hajiya Rabi Madawaki a gaban uwargidan gwamnan, Hajiya Huriyya Dauda ta fito da wata hanya ta daban amma ta tursasa goyon baya domin zaɓen gwamna Dauda Lawal tilas”. APC ta ci gaba da cewa
