Ofishin NAHCON a Makkah ya duba tsarin rumbun abincin maniyyata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na tabbatar da nasara a aikin hajjin bana, Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta gudanar da atisaye na musamman a rumbun abincin maniyyata a ofishin Rawaf Mina dake Makkah.

An yi hakan ne domin duba nagarta da inganci wajen cin abincin maniyyatan Nijeriya a karkashin kulawar jami’ai na musamman.

A sanarwar da jami’in hulďa da jama’a na hukumar a Makkah, Muhammad Ahmad Musa ya fitar, Shugaban NAHCON, Farfesa Sale Abdullahi Usman, wanda mataimakin kodinetan hukumar a Makkah, Alidu Shitu ya wakilce shi, ya jagoranci tawagar zuwa wajen rumbun abincin.

Ya bayyana cewa, nagarta da adadin abincin gami da ďanďanonsa ya yi daidai da abinda zai gamsar da maniyyatan a yayin gudanar da abadunsu.

Da ya ke jawabi, Shugaban Rawaf Mina Zuhaer A. Sadayu ya tabbatar wa jami’an NAHCON cewa an naďa jami’in kula da harkokin abinci da zai sanya ido kan dukkanin matakan yayin ciyarwa ga maniyyatan.

By Babaji