Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin cewa matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka na kwace fili da rushe ginin Asibitin zamani da kamfanin “Tiamin Multi Serɓices Global Limited” ke ginawa a unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, a ƙaramar hukumar Tarauni, ya saɓawa doka.
Kotun ta umarci Gwamnatin jihar ta biya kamfanin diyya ta Naira biliyan 2.635 sakamakon wannan take haƙƙin kamfanin.
Kotun ta ce gwamnatin da ta gabata a ƙarƙashin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta ƙwace filin tare da rushe gine-ginen da aka kusa kammalawa a wancan lokaci.
Kamfanin “Tiamin “ya shigar da ƙara tun a watan Oktoba na shekarar 2019, yana neman diyya kan abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙiin mallaka da rushe asibitinsa ba tare da bin ƙa’idar doka ba.
A hukuncin da Mai shari’a Ibrahim ƙaraye ya yanke a ranar Laraba, kotun ta bayyana cewa kwace filin da Gwamnatin Kano ta yi a ranar 3 ga Nuwamba, 2021, ta hanyar wasiƙa daga Hukumar Kula da Filaye ta Jihar Kano, ya saɓa da kundin tsarin mulki da kuma dokar mallakar fili ta ƙasa.
Mai shari’a ya jaddada cewa Gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne ba tare da bai wa kamfanin damar kare kansa ba, lamarin da ya sa kwace filin da kuma rushe ginin suka zama babu inganci a doka.
Kotun ta kuma ta soki gwamnatin jihar bisa matakin rushe ginin a yayin da ƙarar ke gaban kotu, tana mai bayyana hakan a matsayin saɓa wa doka.
