Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tun bayan samun tangarɗar na’urori da hukumar JAMB ta ce an samu wanda ya wanda ya shafi sakamakon jarrabawar UTME na ɗalibai sama 300,000, zarge-zarge suka fara bayyana cewa an yi samu tangarɗar ne da gangan domin a kada ɗalibai ‘yan ƙabilar Igbo da ke rubuta jarrabawar.
A yayin da wasu ke yaba wa hukumar JAMB saboda amsa laifin kuskuren da aka samu, wasu sun zargi hukumar da nuna son kai tare da neman shugaban hukumar, Is-haƙ Oloyede, wanda farfesa ne, da ya ajiye aikinsa.
Wasu kuma sun yi wancan zargi na cewa an yi komai da gangan ne saboda a kada da ɗaliban da suke yankin Kudu maso gabas.
Sai dai wasu majiyoyi daga hukumar JAMB sun shaida wa Manhaja cewa wannan zargi ba lallai ne ya zama gaskiya ba, saboda mafi yawa na ma’aikatar da ke kula da fitar da sakamakon jarrabawar ‘yan Kudu maso gabas ne.
Majiyar ta kuma bai wa Manhaja wasu daga cikin sunayen jami’an da suke daga yankin kudu maso gabas da suka haɗa da shugaban sashen kula da kimiyyar sadarwa ta zamani (IT).
Majiyar wacce ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce, wancan zargi bai da tushe balle makama.
Majiyar ta ce, hatta babban jami’i mai kula da masu aikin samar da harkokin sadarwar ɗan ƙabilar Igbo ne daga jihar Delta mai suna Jeffrey Onochi.
“Shi ne yake kula da harkar fidda sakamakon na JAMB. Shin kana nufin za a haɗa baki da shi a kada da ‘yan ƙabilar Igbo kenan?” inji majiyar tamu.
Sannan Manhaja ta rawaito yadda aka samu wasu ‘yan ƙabilar Igbo da ke cikin tawagar da aka ɗora wa nauyin gyara matsalar tangarɗar da ta shafi jihar Legas da yankin kudu maso gaba ɗin.
Wasu daga ciki da majiyar tamu ta bayyana mana sunayensu sun haɗa da: Stanley Agu daga Imo da John Chima Iheonu daga Abia.
Sannan mutane biyu da ke sa-ido kan jarrabawar JAMB na jihohin Legas da Owerri – Uche Ohielo da Collins Ojiere – sun fito ne daga yankin Kudu maso gabas.
Haka kuma daraktan da ke kula da ofishin hukumar na shiyyar Owerri ‘yar ƙabilar Igbo ce mai suna Gloria Anyaegbu daga jihar Anambra.
“Ba zai taɓa yuwuwar waɗanann mutane su ci dunduniyar ɗaliban da suka fito daga yankinsu,” a cewar majiyar tamu yana mai bayyana zargin da rashin hankali.
Ya ce, “Ma’aikatan JAMB suna aiki ne da ƙwarewa ba wai amfani da ƙabilanci ko siyasa ko addini da makamantansu ba.”
Game da tangarɗar da aka samu:
Ranar Larabar makon da ya gabata ne, shugaban hukumar JAMB, Oloyede, ya bayyana cewa tangarɗar da aka samu ta shafi sakamakon ɗalibai 379,997 da suka yi jarrabawa a cibiyoyi 157 a jihar Legas da yankin kudu maso gabas.
JAMB ta gano tangarɗar ce bayan ta yi gaggawar nazarin sakamakon na 2025 da kuma nuna damuwa game da faɗuwar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar duk da ƙwazon da suke da shi.
Daga nan ne JAMB ta bincika ta kuma gano cewa matsalar ta shafi ɗalibai 379,997 cikin ɗalibai 1.9 da suka zauna jarrabawar.
A cewar JAMB matsalar ta shafi shiyyoyin Lagos da Owerri, wato jihar Legas da kuma shiyyar Owerri – Anambra, Imo, Abia, Ebonyi, da Enugu.
Kuma tangarɗar ta shafi cibiyoyin rubuta jarrabawa 65 ne a jihar Legas da 92 daga shiyyar Owerri.
Sannan hukumar JAMB ta sake bai wa ɗaliban damar sake rubuta jarrabar ga ɗaliban da abin ya shafa.
Game da zarge-zargen da aka yi:
Akwai fitattun ‘yan Najeriya da sauran masu amfani da kafafen sada zumunta da suka yaɗa labaran matsalar da aka samu na na’ura kan cewa an yi ne don kada ɗaliban da suka fito daga yankin Kudu-maso-gabas – jihohin Igbo.
Ga misali, ƙungiyar matasa ‘yan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze (OYC) ta zargi hukumar JAMB da shirya wannan tangarɗa wanda ya jawo faɗuwar ɗalibai da yawa daga yankin kudu maso gabas musamman ɗalibai ‘yan ƙabilar Igbo.
Shi ma shugaban ƙungiyar malaman jami’ar reshen jami’ar Nsukka (UNN) Óyibo Eze, ya yi irin wancan zargi na tale ƙafafun ɗaliban da suka fito daga yankin kudu maso gabas.
“Gwamnatin Najeriya yanzu ta dawo wani sabon salon bi-ta-da-ƙulli ga ‘yan ƙabilar Igbo ta hanyar dakile cigaban ‘ya’yansu ta amfani da hukumomi kamar JAMB don tauye su,” in ji wani fitacce ɗan kare haƙƙin bil’adama Omotayo Williams, ta shafinsa na ɗ (@KadunaResident).
Haka ma wani mai suna Ben, ya ce, “Abin da JAMB ta yi tana sane ta yi shi kan ‘yan ƙabilar Igbo. Jihar Legas ba a so ta faɗa cikin matsalar ba.”
Sai dai hukumar JAMB ta mayar da martani a yayin da take amsa tambaya daga Manhaja a ranar Laraba kan waɗancan zarge-zarge.
“Zargin da ake yi ba gaskiya ba. Zan iya gaya maka cewa abin da shugaban JAMB ya faɗa game da tangarɗar da aka samu gaskiya ce. Amma ba wani zargi cewa an nemi taɗe ƙafar ‘yan ƙabilar Igbo. Wannan zargi ne marar tushe,” a cewar wani jami’in hukumar ta JAMB.
