Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta ce ta kama wani boka bisa zargin mallakar makamai da harsasai a Unguwar Ugwuochie-Iwollo, karamar hukumar Ezeagu ta jihar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun gano bindiga ƙirar gida, bindigar reɓolɓer, harsasai guda 38.
Ndukwe ya ce an kama wanda ake zargin ne ta hannun jami’an rundunar musamman masu yaki da ƙungiyoyin asiri (SPACS).
Ya ƙara da cewa bokan, wanda za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike, ya amsa cewa shi mamba ne na ƙungiyar asiri ta Black Aɗe.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mamman Giwa, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da kiransu da su tabbatar da cewa “jihar Enugu ta kasance wuri mai wuya ga masu aikata laifi da ba su da niyyar tuba.”
