Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ƙaramin Minista a ma’aikatar tsaron Nijeriya Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya sake tabbatar da ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gina masana’antar ƙera kayan tsaro mai ƙarfi a cikin gida, domin biyan buƙatun tsaron ƙasa da kuma cimma burin dogaro da kai wajen samar da kayan aikin soja.
Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin wata ganawa da wata tawaga daga kamfanin fasahar tsaro, D7G Limited, a hedikwatar tsaro da ke Abuja, inda ya jaddada muhimmancin rage dogaro da ƙasashen waje, wajen sayen kayan inganta tsaro.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kamfanin D7G Limited, Mr Osman Chennar, na daga cikin shirin ci gaba da tuntuɓar masana’antun ƙera kayan tsaro da aka sahale musu aiki a cikin gida, da nufin ƙarfafa ikon samar da kayan tsaro a cikin ƙasa, bisa manufar gwamnatin tarayya ta masana’antar ƙera kayan tsaro ta cikin gida.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na kafafen yaɗa labarai, Ahmed Dan-Wudil, ya fitar, Matawalle ya yaba wa Kamfanin D7G Limited kan yadda ya zuba jari a fannin samar da kayan aikin tsaro a cikin gida.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da burin bunƙasa masana’antun ƙera kayan aikin soja na cikin gida domin tabbatar da ‘yancin kai a fannin ƙera makamai, jigilar su da kuma kula da tsarinsu.
D7G Limited na daga cikin mambobin ƙungiyar Masana’antun ƙera kayan samar da tsaro ta Nijeriya DIAN, kuma ya ƙware a bincike, ƙerawa da haɗa tsarin kayan aikin soja masu inganci.
Ayyukan kamfanin sun yi daidai da manufar gwamnatin tarayya na gina ingantacciyar masana’antar ƙera kayan samar da tsaro da za ta iya magance ƙalubalen tsaron ƙasa.
Matawalle ya sake jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na da niyyar yin aiki tare da kamfanonin da suka cancanta a fannin tsaro domin ƙarfafa ƙarfin cikin gida, alamar da ke nuna sabuwar matsaya ta dogaro da kai a fannin tsaro na ƙasa.
