
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓe na 2027 saboda ba shi da burin hakan.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan yaɗa labaransa, Michael Ohiare, Yahaya Bello ya ce ya yi mamakin ganin wani bidiyo na gangaminsa dacke yawo wand tun a shekarar 2022 aka yi, inda ake yaɗa shi da sunan zai yi takara a matsayin abokin karawar Shugaba Bola Tinubu.
Ya kuma ce, duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya, Shugaban ƙasar da ƴan tawagarsa sun yi wa ƙasar ƙoƙari, yana mai jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen 2027.
Ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi watsi da bidiyon da ake yaɗawar, wanda ya ce an fito da shi ne da nufin ruďar da al’umma.
Ya ƙara da cewa, bidiyon yana ƙaryata waɗanda suke yaɗa shi domin a jikin allunan da aka yi rubutu akwai 2022, inda ya ce masu ƙoƙarin ganin sun kai shi ƙasa ne suke yaɗawa, yana mai kara jaddadagoyon baya ga Shugaba Tinubu.
