Daga AISHA ASAS
Masana’antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, ta fada cikin yanayin alhini da jimami bayan da aka tabbatar da rasuwar fitattun ma’aikatan kamara guda biyu, Johnson Onoriode Ododife da Chigo Gozman, sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru, yayin da suke dawowa daga bikin aure a birnin Port Harcourt.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya auku ne da daddare, inda motarsu ta kauce wa hanya ta bugu da bishiya. Kafin isowar jami’an agaji, an tabbatar da mutuwar dukkansu. Hukuma na ci gaba da bincike kan musabbabin hatsarin, yayin da ake ta ƙorafe-ƙorafe game da lalacewar titunan Najeriya.
Sanannun ‘yan fim da daraktoci sun cika kafafen sada zumunta da saƙonnin ta’aziyya. Darakta Toka McBaror ya bayyana su da kalmar “tushe a bayan kyamara”, yayin da jaruma Rita Dominic ta rubuta cewa, “Kyamararsu na bada labari fiye da murya. Nollywood ta rasa haske.”
Johnson Ododife mai shekara 35, ya shahara wajen ɗaukar finafinai masu zurfin tunani da soyayya, kuma kwanan nan ya kammala aiki da Netfliɗ Nigeria. Chigo Gozman mai shekara 31, ya kasance masanin ɗaukar finafinai masu cike da tasiri. Dukkansu na cikin sabbin jaruman da suka ke da nufin sauya salon fasaha a Nollywood.
Rasuwar ta ƙara janyo muhawara kan irin hatsarin da masu ɗaukar finafinai ke fuskanta a tafiyarsu na nesa ba tare da isasshen hutawa ko matakan tsaro ba. ƙungiyar ma’aikatan kyamara ta yi kira da a duba tsarin walwala da hana tafiye-tafiyen dare.
Iyalansu sun sanar da shirye-shiryen jana’iza da za su gudana a Lagos da Asaba, yayin da masoya da abokan aiki ke shirya gagarumin taron tunawa da su ta kafafen sada zumunta da taken #LensOfLegends.
