Rundunar sojoji ta tsare babbar jami’a bisa laifin sata da rashin ladabi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar Sojojin ƙasa (NA) ta ce ta tsare wata babbar jami’a mai suna Koporal Amina Maidoki biyo bayan zargin ta da hannu a sata da rashin ladabi a aiki.

Daraktar Hulďa da Jama’a ta riƙon ƙwarya ta rundunar, Laftanal Kanal Appolonia Anele ta faɗi hakan a wata takarda, inda ta ce tun da daɗewa aka fara bincike akan jami’ar bisa hannu a aikata laifukan waɗanda sun saɓa wa dokokin rundunar.

Haka kuma, ta ce an tsare ta ne a ƙarƙashin dokokin gudanar da harkokin jami’an sojoji, wanda mataki ne na yin adalci a gare ta da rundunar.

Ta ƙara da cewa, duk da cewa an tsare Amina Maidoki, hakan bai sa an tauye mata ƴanci ba, waɗanda daga ciki akwai kula da ɗaukar ɗawainiyarta yadda ya dace.

Bugu da ƙari, rundunar ta musanta dukkan wani zargi na tsare wanda ake zargi ba bisa ƙa’ida ba ko hana wakilci na shari’a kan batun, tana mai cewa an ƙirƙire su ne domin ruɗar da al’umma.

Ta ce, za a fitar da sakamakon binciken da ake gudanarwa akan mai laifin a lokacin da ya ce, don haka jama’a su ƙaurace wa labaran ƙarya da ake yaɗawa game da lamarin.

By Babaji