
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Sakataren Gwamnatin Amurka, Marco Rubio ya umarci a dakatar da bai wa ɗalibai damar neman biza.
Sabon hukuncin ya shafi ɗaliban ƙasashen waje ciki har da na Nijeriya, wanda kuma kaso ne mai girma na kuɗaɗen shiga da jami’o’i ke samu, lamarin da ya sa gwamnatin ta haramta wa Jami’ar Harvard ɗaukar ɗaliban da ba ƴan ƙasar ba a makon da ya gabata.
Wannan hukunce zai haifar da tsaiko ga matasan ƴan Nijeriyar da ke fita waje da nufin neman ayyuka masu gwaɓi a nahiyoyin Turai, Amurka, Asiya da wasu sassan duniya musamman a ƙasashen Amurka, Birtaniya da Kanada.
A sanarwar da Sakataren ya fitar, kamar yadda AFP ta ruwaito, gwamnatin ta umarci ofisoshin jakadanci da na tuntuɓa da kada su sake bai wa wani ɗalibi biza ko na damar samun aiki daga yanzu har zuwa lokacin da za a sake fitar da wani jawabi daga gwamnati akan batun.
Sanarwar ta kuma ce, akwai shirin bada tsare-tsaren da za bi wajen neman biza ga ɗaliban da aka bai wa damar hakan ta Soshiyal Mediya.
Sanarwar, wadda ake kira da ‘Cable’ ta ƙara da cewa, akwai yiwuwar dakatarwar ta zama na lokaci ƙanƙani, ya na mai faɗa wa ofisoshin jakadancin cewa za su samu sabon tsari daga gwamnati nan ba da jimawa ba.
