
Daga BELLO A. BABAJI
Wani hari cikin dare ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ƴan gida ɗaya a Ƙauyen Kopmur dake Gundumar Mushere a Ƙaramar Hukumar Ɓokkos ta Jihar Filato.
Wani mataimaki ga shugaban ƙaramar hukumar da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce mutane shida ne aka kashe ba bakwai ba.
Haka ma wani jagoran matasa mai suna Kopmut Monday ya bayyana cewa, maharan sun farmaki ƙauyen ne cikin dare, inda suka shiga wani gida tare da kashe mutane bakwai, lamarin da ya sa ƴan sanda suka garzaya yankin.
Harin ya auku ne ƙasa da kwana ɗaya da ƴan bindiga suka harbe Rebaran Mikang Lekyil na cocin COCIN LCC a Ƙauyen Kwakas na Ƙaramar Hukumar inda wasu mata biyu suka raunata a yayin al’amarin.
An kashe jagoran addinin ne biyo bayan zargin ƙone wasu gidaje a Dingak, wanda yanki ne na ƙabilar Fulani.
