‘Yan bindiga sun sace mutum 117 da hallaka wasu tara a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka aƙalla mutum tara sannan kuma suka yi awon-gaba da wasu magidanta 117, a garin Danmuntari da ke yankin Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Wasu mazauna garin da suka tsira daga harin sun tabbatar wa da BBC, da cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 27 ga watan Mayun, 2025, lokacin da ‘yan bindigan su ka yi wa garin ƙofar-rago.

Daga cikin waɗanda ɓarayin dajin suka kashe har da wata mata mai jego da jaririnta, inda suka harbe su tare da sauran jama’ar da suka hallaka ta hanyar harbin kan-mai-uwa-da-wabi a lokacin da suka shiga garin, kamar yadda shedun suka yi bayani.

”Da la’asar ɓarayin suka kewaye garin suka dinga harbe-harbe wanda hakan ya sa dole mutanen garin suka watse suka cimma na kashewa, suka kashe mutum tara,” inji ɗaya daga cikin mutanen garin.

Ya ƙara da cewa, ”Abin ban tausayi akwai mace ɗaya da ba ta wuce sati biyu da haihuwa ba suka kashe ta da ita da jaririnta.”

Haka shi ma wani daga cikin mutanen garin wanda a yanzu yake gudun hijira a garin Baina ya tabbatar wa BBC harin da ‘yan bindigar suka kai musu.

Mutumin ya ce suna zaune kawai suna shirye-shiryen ayyukan gona da sauran ayyuka, sai kawai suka ga ‘yan bindigan suna ta shigo musu gari ta kowane ɓangare a kan babura.

”Sun shigo garin wasu ta gabas wasu ta yamma, wasu ta kudu wasu ta arewa, suna ta harbe-harbe, sun ɗauki wasu magidanta 117, sun cimma wata mata tana jego, sabuwar haihuwa, sun kashe ta da ita da jaririnta, bayan sauran wasu bayin Allah da suka kashe kimanin mutum tara dai suka kashe,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, ”babu wani sakamako da muka samu daga hukuma. Mu muna tunaninma, mu ‘yan jihar Kebbi ne ko ma wace jiha muke?

”Babu ɗauki babu wasu jami’an tsaro da aka taɓa kawo mana don su tabbatar mana da tsaro a inda muke zaune, babu wani sakamako da ya zo daga hukuma ko kuma a kan ɓarayin nan, babu dai wani bayani,” ya yi ƙorafi.

Bayanai dai sun nuna cewa tun bayan kai harin al’ummar garin na ta watsewa, inda wasu ke nufar jihar Zamfara wasu na tafiya Kebbi.

Al’ummar garin sun ce wannan shi ne karo na uku da ‘yan bindigan ke kai musu hari, inda suke zuwa da yawa a kan babura suna ci musu zarafi da kuma kisa.

Duk wani ƙoƙari da Manhaja ta yi na ji daga bakin hukumomin tsaro na jihar ta Kebbi a lokacin haɗa wannan rahoto ya ci tura.

Al’amarin tsaro dai a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta Nijeriya da ma wasu sassan ƙasar na ci gaba da ta’azzara, duk da yadda hukumomin ƙasar ke cewa suna ƙoƙarin shawo kan matsalar.

By ukarofi