Gwamnan Neja ya ƙaddamar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya 20

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya ƙaddamar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 20 da aka gina a ƙananan hukumomi 16 a jihar.

Bago ya ce waɗannan cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin guda 100 din da shirin NG-CARES wanda ke ƙarƙashin hukumar raya al’umma CSDA dake jihar ke ginawa.

Ya ce nan ba da daɗewa ba za a kammala gina wasu cibiyoyin kiwon lafiya 40 a jihar inda yake cewa gwamnati ta ware isassun kuɗaɗe a Asusun inganta fannin lafiya.

“Gina waɗannan asibitoci na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ganin ta inganta fannin lafiyar jihar.

“Duk Cibiyar lafiyar da ta yi ƙoƙari wajen kulawa da marasa lafiya da adana kayan aiki da gine-ginen asibitin za ta samu tukwicin naira miliyan biyar duk wata.

Za a ƙara karrama wasu fitattun mutane uku saboda jajiircewarsu wajen inganta fannin lafiya a jihar ta hanyar saka sunayensu a wasu asibitocin da aka gina da suka hada da cibiyar Maitumbi bayan marigayiya Hajiya Zainab Yakubu Garba, asibitin dake titin Peter Sarki bayan Marigayi Peter Sarki, da kuma cibiyar Anguwan Daji uwargidan gwamnan Hajiya Fatima Umaru Bago.

Shugaban ƙungiyar CSDA A’isha Abdulkadir ta yaba da ƙoƙarin da gwamnan ke yi wajen inganta fannin lafiya a jihar.

Aisha ta ce iyalin marigayi sanata Idris Kuta sun yi alkawarin ɗaukar nauyin saka mazauna karkara 100 cikin tsarin inshorar lafiya na jihar.

Kwamishinonin raya karkara Phalalu Bako da raya Cibiyar Kiwon Lafiya na Matakin Farko Ibrahim Dangana da su hada hannu wajen ganin an inganta aiyukkan cibiyoyin lafiyar domin ganin mutanen sun ci gaba da samun lafiya ta gari a jihar.

By ukarofi