Yadda jama’ar gari suka kashe DPO, suka ƙona ofishin ’yan sanda a Kano 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta.

Fisatattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Ranon hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan.

Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare.

Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin danganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi.

Sanarwar ta bayyana cewa, wanda aka kama din wani makaniken babur ne wanda ƙorafe-ƙorafen jama’a suka yi yaw a kansa.

Ya ce, a yayin da yake tsare, ya nuna alamun rashin lafiya inda aka kai shi babban asibitin Rano, inda ya mutu da safiyar ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 6:00 na safe.

A sakamakon haka, wasu gungun fusatattun mutane suka kai hari a hedikwatar ’yan sanda ta Rano, inda suka cinna wuta a wasu sassan ofishin, suka lalata motoci goma, sannan suka ƙona wasu biyu.

By ukarofi