Sojoji sun halaka mayaƙan ISWAP da dama a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dakarun sojojin Nijeriya sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan.

Majiyar leƙen asirin hedikwatar sojan Nijeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:35 na wayewar safiyar talata 27 ga watan Mayu.

Majiyar ta ce wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadin su ba sun kai hari a bataliya ta 50 da ke Marte.

Dakarun da ke samun goyon bayan wata tawaga ta runduna ta 24 da bataliya ta musamman ta 134, sun yi gaggawar fafatawa da ’yan ta’addan a wani ƙazamin faɗan da aka kwafsa.

A cewar rahoton, dakarun rundunar sojojin saman Nijeriya na Operation Haɗin Kai, ta aiwatar da aikin leƙen asiri ta sama, da kuma ɗauki ba daɗi, wanda ya taka rawar gani wajen fatattakar ’yan tada ƙayar bayan da suka tsere.

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar daƙile harin tare da dawo da cikakken iko a yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin zaƙulo abubuwan da suka rage da kuma ƙwato makamai da kayan aikin da ’yan ta’addan ke amfani da su.

“Sojoji biyu sun rasa ransu a yayin wannan farmaki, sannan an samu wasu asarorin kayayyakin da suka hada da lalacewar wata babbar mota mai ɗauke da bindiga da kuma tayar wata motar sojoji,” inji majiyar.

Harin na baya-bayan nan a Marte na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke dada kai hare-hare a yankin tafkin Chadi da arewacin Borno, inda ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram suka yi yunƙurin sake kafa sansanoninsu.

A halin da ake ciki dai, ana ci gaba da sanya ido sosai kan harkokin tsaro a jihar Borno, inda ake ci gaba da gudanar da sintiri da tattara bayanan sirri da nufin hana kutse a nan gaba, inji majiyar ta sojan Nijeriya.

By ukarofi