Sojojin sama sun samu ƙarin alawus

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta sanar da ƙarin kashi 100 cikin 100 na kuɗin abinci da ake baiwa jami’anta, a wani yunƙuri na ƙara ɗorewar ayyukan soja da walwalar ma’aikata. Babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sabuwar matsugunin ma’aikata 160 a Sam Ethnan Air Force Base, Legas.

Bayanin da aka fitar a ranar Lahadi ya ce ƙarin kuɗin abincin na cikin kasafin kuɗi na shekarar 2025 tare da ƙaddamar da sabbin manufofin inshora, rarraba sabbin kayan sawa da kuma ƙarin tallafin lantarki ga ma’aikatan sansanin. Hakanan, an kammala wasu muhimman ayyuka na kiwon lafiya da gina sabbin cibiyoyi.

A cewar Air Marshal Abubakar, an riga an biya diyya ga jami’ai 23 ƙarƙashin sabon tsarin inshorar haɗurra, inda aka biya guda tara cikin makonni da suka gabata. Ya bayyana cewa inshorar na taimakawa wajen kula da raunuka, rashin lafiya, mutuwa, da biyan albashi yayin da jami’i ke jinya.

Hakanan, rundunar tana gudanar da ayyukan gine-gine sama da 470 a faɗin ƙasa, ciki har da gidajen zama, asibitoci, wuraren ibada, da filayen motsa jiki. Air Vice Marshal Adeniran Ademuwagun ya yaba da jajircewar shugabanci na CAS, yana mai cewa ayyukan za su ƙara ƙaimi da ƙwazon jami’an rundunar.

By ukarofi