Shekaru biyu na Gwamna Ɗanmodi kan karagar Jigawa, taya murna da hannunka mai sanda

Spread the love

Daga MUHAMMAD ABUBAKAR TAHIR a Haɗeja

Bayan gaisuwa mai yawa tare da taya murna ga Mai Girma Gwamna bisa cikarsa shekaru biyu akan karagar mulki, Ina fatan Allah ya ci gaba da yi maka jagora a sauran shekaru biyu da suka rage da ma wanda kake fatan samu a nan gaba.

Haƙiƙa Mai Girma, duk wanda yake bibiyar tafiyar mulkinka a cikin shekaru biyun nan, dole ya yi maka adalci, domin ka cancanci a yaba maka ta ɓangarori da yawa kama da kiwon lafiya, tsaro, noma, ayyukar karkara, walwalar ma’aikata, ilimi da sauran ɓangarori.

Daga cikin abin da ya ja hankalina kan salon mulkinka har da yadda ka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da biyan ma’aitakan jiharmu mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, wanda ka ninka musu ba tare da ɓata lokaci ba. Ka cancaci a yaba maka da sauran ɓangarorin waɗanda na san mai karatu zai yi wa kansa adalci wajen zayyano wasu a ɗuciyarsa.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, Mai Girma Gwamna ya zama dole a riƙa sara ana duban gatari. Haƙiƙa gwamnatinka akwai matsaloli bila adadin, waɗanda kusan za mu iya cewa, sun hana ruwa gudu ko kuma akwai sauran rina a kaba.

Ni ɗan jarida ne, wanda nake bibiyar ayyuka a birni da karkara, na kuma sani babu yadda saƙona zai kai gare ka idan ba ta wannan hanyar ba, duba da ci gaban jiharmu shine babban burin dukkan mai son tabbatar da adalci a gwamnatin dimukraɗiyya.

Mai Girma Gwamna, haƙiƙa asibitocinmu na ƙauyuka da ma birane cike suke da ƙarancin magunguna, inda na shaida yadda ma’aikatan dake karɓar magani a Tsarin Inshorar Lafiya Na Jiha (JICHMA) ke koka wa da ƙarancin magunguna masu tasiri da inganci. Duk da sauƙi, wasu sun gwammaci su fita wajen asibiti su sayi magani, domin ya fi musu, don lallai babu biyan buƙata. Haka kuma ƙarancin ma’aikatan lafiya yana barazana ga rayukan al’ummar jiharmu, inda ’yan kwanaki aka jiyo sababbin maikatan jinya da unguzoma suna ƙorafin rashin ɗora su akan tsarin albashi na Naira 70,000 da aka yi.

Mai Girma Gwamna, jiharmu na samar da kaso 75 cikin 100 na abinci da ake ci a faɗin jihar, kamar yadda Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana, haka kuma kashi 90 na al’ummar jiharmu manoma ne, waɗanda sun dogara kacokam ga noma wajen rayuwarsu. Sai dai kuma mu da muke cikin manoman na karkara da ke fitowa a lokacin zaɓe su zazzaga maka ƙuri’a na ƙorafin tallafin kayan amfanin gonar da ake badawa ba ya isa gare su. Wani lokacin sun gwammaci su karɓi bashin ƙungiyoyi da su jira na gwamnatin, wanda babu tabbacin samun sa. Ina da tabbacin yadda Gwamnatin Tarayya ta ke alfahari da manoman Jihar Jigawa da za a tallafa musu a riƙa bi langu da saƙo, da abincin da za a fitar a cikin shekaru biyu sai ya samar wa ƙasa abinci mai yawa tare da samarwa matasa aikin yi.

Mai Girma Gwamna, gwamnatin na ƙoƙari wajen ɗaukar matasa aikin yi, inda ka bayyana cewa, ka ɗauki matasa sama da 3,000 aiki ta shirin J-Tech, amma haƙiƙa da yawa daga cikin makarantun na fuskantar ƙaranci malamai, kayan aiki, da ma guraben karatu mai nagarta. Mai Girma Gwamna, akwai ɗaruruwa matasa da suka kammala karatu tun daga matakin NCE, difloma, digiri, digiri na biyu (masters) da sauransu, waɗanda suke da ƙwarewa a ɓangarori daban-daban da za su iya tallafa wa jihar wajen kai ta mataki na gaba, da yawansu suna gararamba a titina babu abun yi. Haka kuma rashin aikin yi ya saka su koma wa gida suna fafutukar nema wa kansu mafita. 

Ko shakka ba na yi akwai ɗaruruwan guraren ayyuka wanda wasu sun yi ritaya, wasu sun rasu, da ma ma’aikatan bogi 6,000 da mai girma gwamna ya ce sun bunkaɗo, wanda da Mai Girma Gwamna zai duba lamarin da an maye gurbinsu da matasan da ke tsammanin samun cin gajiyar wannnan gwamnatin da ta ke fatan dawowa a mulki a zango biyu. 

Mai Girma Gwamna, duk da ka sani Ina daɗa tunasar da kai cewa, matasa dai su ne tushen sauyi, su ne kuma kowacce al’umma ta ke fatan gina su, domin samar da gobe mai kyau. Bai kamata a riƙa wasa da goben matasan jiharmu ba, a riƙa jawo su jiki ana tafiya da su, domin don tuwon gobe ake wanke tukunya. Ba kuma iya matasan da suka yi karatu ba, akwai ɗaruruwan matasa da suke sana’o’i daban-daban kama daga gyaran waya, ɗinki, adadaita sahu da sauransu, waɗanda suke buƙatar tallafi kama na kuɗi, koyar da sana’a da ma sauran muhimman abubuwa waɗanda za su taimaka musu wajen cigaban rayuwarsu da ma iyalansu gaba.

Jiharmu na daga cikin johohin da Allah ya kare daga aikata manyan laifuka, kamar harin ’yan bindiga, sace-sace da shaye-shaye. ɗauke wa matasa hankali da sana’o’i shine hanya mafi sauƙi wajen raba su da aikata miyagun ayyuka. Ko a kwanakin bayan na yi hira da wasu matasa da ke sana’o’i daban-daban, inda suka bayyana cewa, suna buƙatar agaji daga gwamnatin jihar, amma har yanɗu kokensu bai kai ga gwamna ba.

Mai Girma Gwamna, ana yi maka laƙabi da ka na kan daidai, amma lallai wasu daga cikin makusantanka na shafa maka kashin kaji wajen fito da matsolin fili har ma masu sa ido da bibiya su gani su yi sharshi a kai. A nan na ke kira da Mai Girma Gwamna da ya riƙa karɓar koken al’ummar kai-tsaye a shirin gwamnatin da jama’a suka zaɓa, kuma ka tabbatar an yi abinda ya dace, domin ko yanɗu gwamna na fatan sake dawowa mulki a karo na biyu.

Ni ba ɗan siyasa ba ne, ɗan jarida ne wanda kullum ba ni da buri da ya wuce a ce jiharmu ta kai ta wuce takarorinta da Janar Babangida ya ƙirƙiro su, wanda dukkaninsu za su cika shekaru 34 nan da ’yan watanni. 

A ƙarshe, Ina kira ga Mai Girma Gwamna ya yi wa kalamaina kallo na basira, domin yin abinda ya dace a lokacin da ya dace, domin gangar siyasa na daɗa ƙuratowa kuma dai burin kowane ɗan siyasa shine al’umma su cigaba da mara masa baya, domin daɗewa karagar mulki a karo na biyu. Na barka lafiya.

Muhammad Abubakar Tahir ɗan jarida ne daga Hadejia a Jihar Jigawa

By ukarofi