Fate-fate ake tonawa… amma ba tuwon laushi ba

Spread the love

Daga UNCLE LARABI 

Waɗannan sune iyayen gidana a tafiyar siyasar Kwankwasiyya; Sanata Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Mai Girma Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf. Bayansu a tafiyar Kwankwasiyya ba ni da wani ubangida sai dai waɗanda na sani suka san ni, suka kuma san Ina tafiyar Kwankwasiyyar ko kuma ma ba su sani ba. Akwai irinsu; Hon. Akibu Isa Murtala SA, Hon. Ismail ɗanmaraya Kwamishinan Kuɗi, Hon. Sani Igwe SA, Hon. Amb. Jamilu Bala Gama, Hon. Baba ɗantiye  Kwamishina ɗattijon arziki maras girman kai da mutunta ɗan adam, Fauziyya D. Sulaiman  SA Uwar Marayu (na ma riga ta shiga Kwankwasiyyar, amma ta fi ni sa’a a cikin Kwankwasiyyar) da sauransu da dama.

‘For God sake’, na fara jin Ina son tafiya Kwankwasiyya ne tun farkon mulkin Kwankwaso 1999-2003. Ba kuma Ina yi ne don a ba ni kuɗi ko wani abu ba, a’a, Ina yi ne, don a yi wa al’umma aikin da za a gani mu ’yan tafiyar mu fita kunya. A 2019 da 2023 babu wanda zai bugi ƙirji ya ce ya fi kowa yin Kwankwasiyya. Ina jin duk mutanen Kano har da maƙotanmu sauran jihohi ko na ce ma duk Arewa da ƙasashen da ke maƙotaka da mu irinsu Nijar, sun taya mu yin Kwankwasiyya da kuma tallata Kwankwasiyya. Ba na mantawa a lokacin Duk Arewa tamkar Abba Gida-Gida ne kaɗai ɗan takarar gwamna.

Don haka Ina kira ga Mai Girma Gwamna Injiniya Abba K. Yusuf da ya ci gaba da ayyukan alherin da ya ɗauko yake yi, waɗanda dukkan al’umma za su amfana, ba wai kawai ɗaiɗaikun mutane, musamman waɗanda suke kusa da ku ba.

Idan aka ce sai waɗanda suke kusa da ku ne kawai za su amfani gwamnati, to gaskiya akwai matsala kuma za a samu naƙasu, domin kowa a Jihar Kano ya bayar da gudummawarsa a zaɓenka a 2019 da  2023. Kawai wasu irina da yawa ba mu samu damar isowa gare ka ba ne ko kuma isowar ta yi ƙaranci, ga kuma mutane da yawa, don haka ba ma za ka iya gane fuskokinmu ba ko da an tuna maka. 

Sannan akwai waɗanda suke kusa da kai ɗin da su kuma ba sa shiri da wasu masoyan naka. Kuma ba wai shiri ne na siyasa ba, a’a, kawai na ‘personal Interest’ ɗinsu ne ko kuma kawai na rashin haɗuwar jini ne. Don haka idan an ce sai ta hannunsu ne kawai aikinka ko alherinka zai isa ga al’umma za a iya samun naƙasu. 

A ƙarshe, Ina yi maka fatan alheri kai da jagoran wannan tafiyar tamu mai albarka Kwankwasiyya Amana, wato ubanmu, Injiniya (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso. Ina kuma yi wa kaina fatan idan alheri ne, Allah ya sa na samu takarar kujerar Sanata Kano ta Tsakiya ko ɗan Majalisar Tarayya ko ɗan Majalisar Jiha a zaɓen da zai zo na 2027 (IDAN ZA KA ROƙI ALLAH, KA ROƙE SHI DA BABBAN MASAKI, INJI KAKANNINMU NA DA).

Uncle Larabi, wanda ke kira Abdullahi Jibril Dankantoma shine kuma Abdullahi Jibril Larabi, marubuci ne a Kano. Alhamis, 15 ga May, 2025, 08065418892

By ukarofi