Majalisar Wakilai ta titsiye jagororin WAEC bisa matsalolin jarrabawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne Kwamitin Majalisar Wakilai akan Ilimin matakin farko da Hukumomin jarrabawa ya yi wa hukumar gudanarwa ta Majalisar kula da Jarrabawa a Yammacin Afirka (WAEC) titsiye bisa gazawa na matsalolin da ake samu a yayin rubuta jarrabawar SSCE ta bana.

A yayin zaman bincike a majalisa, ƴan majalisar sun titse Shugaban WAEC, Dakota Amos Dangut akan abinda suka kira da gazawar cika aiki, wanda hakan abu ne da zai daƙile yardar al’umma game da hanyoyin jarrabawa a Nijeriya.

WAEC ta samu suka daga ɓangarori da dama a sakamakon rahotannin rashin bin dokoki da gazawar ayyuka a yayin gudanar da jarrabawar.

Lamarin da ya sa iyaye da ƙwararru akan harkar ilimi suka bayyana kaďuwarsu duba da yadda hakan ya rage wa tsarin gudanar da jarrabawar nagarta.

Waɗannan ƙalubalen sun haifar da kiraye-kiraye na a gaggauta gyara al’amuran domin dawo da ƙwarin-gwiwa da yardar al’umma a ɓangaren.

Shugaban kwamitin, ɗan majalisa Oforji Oboku (Bayelsa PDP) ya bai wa ƴan Nijeriya haƙuri bisa tsaikon tare da yin alķawarin za su tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

Ya kuma yi alkawarin cewa za a yi bincike daga tushe domin gano asalin matsalar da ɗaukar matakin gyara gami da tabbatar da adalci akan dukkan waɗanda suke da hannu a kai.

By Babaji