Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙaramin ministan tsaro na ƙasa Hon. Bello Mohamed Matawalle ya raba raguna 3000 ga jama’a da kuma ‘yan jam’iyyar APC a wani ɓangare na bukukuwan salla a Jihar Zamfara.
Da yake jawabi ga manema labarai, yayin rabon ragunan a Gusau yau Laraba, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Tukur Ɗanfulani ya ce, za a bai wa shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi rago 1400 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Ya ci gaba da cewa, za a bai wa manyan ‘yan kwamitin jam’iyyar na jiha da na ƙananan hukumomin APC da dattawa da matasa da malaman addini raguna 1600.
Shugaban jam’iyyar, ya yabawa minista Matawalle bisa wannan karimcin, sannan kuma ya buƙaci waɗanda suka amfana da ragunan dasu yi amfani da raguna a matsayin Layya a lokacin Sallah kamar yadda Allah Ta’ala ya tsara.
Ya kuma bayyana cewa, APC za ta dawo da mulki a 2027 a Jihar Zamfara.
