Yadda cutar damuwa ta iyaye ke shafar yara a gida (2)

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu sannu da jimirin karatun jaridar al’umma, Manhaja, sannunmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako.

A wannan mako, za mu tattauna ɓangaren da ba kasafai ake kallonsa a matsayin matsala ba, ko ma in ce ba kasafai ake iya amincewa da wanzuwarsa ba, musamman ma a Arewacin Najeriya, wato cututtuka irinsu damuwa ko baƙin ciki.

A gidaje da dama, akwai cututtukan da ba su bayyana a ido, amma suna barazana ga zaman lafiyar iyali. Cutar damuwa (anɗiety) da bakin ciki (depression) suna daga cikin irin waɗannan cututtuka. 

Yayin da mutane da yawa ke rayuwa da irin wannan ciwo ba tare da sun ankara ba, duk da hakan bai hana yara shiga hatsari su ma na kamuwa da cutar, ko girban tasirin cutar ga iyali, ko da ba su san sunan cutar ba.

Yadda rayuwar yara ke shiga matsala ta sanadiyyar ɗaya daga cikin alamomin ciwon damuwa, wato yawan yin shiru:

Yaro na iya lura da canjin yanayin gida. Idan uwa ko uba na yawan zama shiru ba magana, yawan kuka, ko rashin jin daɗin abubuwa, yaron zai fara tunanin akwai matsala. Wasu yara suna tunanin su ne suka jawo halin da ake ciki. Wannan tunani na iya hana yaro jin daɗi. Kuma zai iya sa ma shi tunanin ko ba a ƙaunar sa ne, kuma kasancewar sa yaro zai iya aminta da hakan har ta kai shi ga wata matsalar.

Waɗanne irin matsaloli da halayya ne za a iya samu a yaron da ke cikin wannan hali?

Yaron da ke fama da irin wannan rayuwa, wato yaron da iyayenshi ke ɗauke da matsala ta ciwon damuwa na iya zama:

Mai yawan jin tsoro ko damuwa.

Mai yin shiru ko rashin magana da kowa.

Mai yawan yin fushi ko yawaita bugun ƙasa da ƙafarsa.

Mai hana kansa wasa da ‘yan uwansa ko abokai.

Wani lokaci malamai ko makwabta kan yi zaton yaron yana da “matsala”, ba tare da fahimtar tushen inda matsalar take ba.

Yadda cutar damuwa ta iyaye ke hana yaro ƙoƙari a makaranta.

Wani abu da ake yawan gani shi ne: yaro yana zuwa makaranta amma ba ya iya mai da hankali. Zuciyarsa tana cike da damuwa, yana jin nauyi a kai. Karatunsa zai ragu, ko ma ya fara gudun zuwa makaranta gabaɗaya. Wannan na iya shafar makomarsa sosai idan ba a taimaka ba.

Yaro ya zama uba ko uwa a ƙarancin shekaru:

Wasu yara, musamman a gidajen da uwa ko uba ke fama da cutar ƙwaƙwalwa, sukan ɗauki nauyin gida. Su ne ke kula da ƙanensu, dafa abinci, yin wanke-wanke, da tabbatar da komai ya tafi daidai. Wannan nauyi yana hana yaron jin daɗin yarintarsa. Yana girma da jin cewa ba zai iya neman taimako ko yin kuka ba wanda hakan kawai matsalace da za ta kawo tikas gare shi tsayin rayuwa, musamman ma ga mace.

Shiru da ƙyamar maganar ciwon damuwa:

A al’adunmu, ana yawan jin cewa “mutumin da ke da ciwon ƙwaƙwalwa to fa mahaukaci ake kiran sa.” Wannan ra’ayi yana sa iyaye su ɓoye matsalarsu. Su na jin kunya ko tsoro kada mutane su ce suna da “hauka.” Amma wannan shirun yana sa yara cikin wahala fiye da yadda ake tsammani.

Shawarwari da taimakon da zai iya taimakawa a wannan fagen:

Kamar yadda masana suka nuna, akwai hanyoyi da za a taimaka kamar haka:

Tattaunawa: Iyaye su kasance masu magana da ‘ya’yansu cikin gaskiya da sauƙi. Ma’ana duk da ciwon da suke fama da shi, su kasance masu jan ‘ya’yansu a jiki suna masu bayanin halin da suke ciki daidai da shekarunsu, wanda hakan zai fahimtar da su ba laifin su ba ne, kuma zai ba wa iyayen damar amincewa da suna tare da matsala, don haka za su nemi magani. Domin ɗaya daga cikin hanyoyin da mai ciwon damuwa ya kamata ya bi don waraka akwai yarda da yana tare da matsalar.

Neman shawarar likita: 

Akwai likitocin da ke iya ba da taimako kan irin waɗannan matsaloli, waɗanda musamman sun ƙware wurin bayar da taimako kan sha’anin da ya shafi ƙwaƙwalwa. Don haka ta tuntuɓar su ne za a san abinda ya kamata a yi ko a bari don neman lafiya, da kuma yadda za a taƙaita illar ciwon ga ‘ya’ya.

ƙungiyoyi da makarantu:

ɗaya daga cikin cigaban da aka samu ta fuskar matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwa, a yanzu makarantu da yawa na da malamai masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, inda musamman ake ajiye malamar da ke tattaunawa da ɗalibai ‘counselling teacher’, (an fi samun hakan a makarantun kuɗi). don haka yake da kyau idan har akwai ire-iren su a makarantar yaranku, ku janyo hankalinsu kan naku yaran, tare da tattaunawa da su kan matsalar da kuke fuskanta, don su san ta yadda za su taimaka wa ‘ya’yanku.

Haka kuma, akwai ƙungiyoyi da ke taimaka wa iyaye da yaransu ta wannan ɓangare.

Dr. Miriam Ayele, wata likita a fannin kula da yara, ta ce: “Yara na buƙatar su ji cewa ana ƙaunarsu, ana fahimtarsu, kuma ba su da laifi.” Da waɗannan ƙungiyoyi akan samu ƙwararru da za su sanar da ku yadda za ku tafi da matsalar tare da wayar maku da kai kan ababen da ya kamata da wanda bai kamata ba.

Duk da wannan dogon bayani da muka yi kan yadda rayuwar yara za ta shiga gagari idan iyayensu na tare da matsalar ƙwaƙwalwa, hakan ba yana nufin dole sai yaro ya samu matsala a irin wannan yanayi ba. Ko da akwai cutar damuwa a gida, hakan ba yana nufin dole sai rayuwar yaro ta lalace ba. Da taimako, kulawa, ana iya canza labarin. Yaro zai iya girma ya zama mai ƙwarin gwiwa, mai iya kula da kansa da sauran mutane.

Daga ƙarshe, mu fahimci cewa, lafiyar ƙwaƙwalwa na da matuƙar muhimmanci, kamar lafiyar jiki. Idan muka fitar da cutar daga cikin duhu, muka buɗe bakinmu, za mu kare makomar yaranmu da dukka iyalinmu.

By ukarofi